Mu dinga yi wa juna uzuri Dan Allah. Idan kana ganin mutum a Online kodayaushe, hakan ba ya nufin ba shi da aiki ba ne, don haka kar ka yi masa mummunar fahimta.
Marubuci:- M. Kabiru Muhammad
Idan kana aikawa da saƙonni ka ga ba a dawo maka da amsa wato Reply, kar ka yi fushi, saboda ba kai kaɗai ba ne kake tura masa da saƙonni. Don haka ka yi masa uzuri.
Idan kana ganin mutum a Online cikin dare 12:00am,1:30am har zuwa 4:00am ko 5:00am, ka tura masa da saƙonni babu Reply wataƙila bacci ne ya ɗauke su.
Da yawa ba sa sanin lokacin da suke barin wayar akan yanar gizo-gizo wato Internet, musamman masu amfani da wayar Android, amma masu amfani da ƙananan wayoyi to su idan suka bar wayar tasu akan yanar gizo-gizo idan aka ɗan jima tana sauke kanta daga kan yanar gizo-gizo har sai dai idan kai ne ka ci-gaba da amfani da ita.
Dan Allah mu rinƙa kyautata kyakykyawar fahimtar junan mu.
ALLAH ya sa mu dace da dacewarsa Amin ya ALLAH.