Akwai bambanci tsakanin ilimi "Knowledge" da kuma hikima "Wisdom" amma sai dai ba kowa ba ne yake iya tantance su ba.
Marubuci:- Usman Yanmaza
Shi ilimi abu ne wanda ake koya kuma a iya, ko a ƙware bisa maida hankali (rigorous test, practice and learning), ita kuma hikima, hikima ce da Allah yake ba wa mutum kaitsaye koda kuwa ba ya da ilimi.
Ita hikima ba ta buƙatar ilimi saboda akan samu mutane da yawa wanda ba su je makaranta ba amma suna da azanci a abubuwa wanda ko wanda ya je makarantar ma ba zai nuna musu wasu abubuwan ba. To amma a falsafance akwai abin da yake haɗa ilimi (knowledge) da hikima (wisdom) wato shi ne kuma basira "cognitive - ability" wanda shi kuma ƙoƙarin ƙwaƙwalwa ne wajen yin amfani da abubuwa.
Sannan kuma akwai bambanci tsakanin mutum mai hikima (wisdom) wanda kuma har yanzu yana da ilimi (knowledge) da kuma wanda yake da hikima amma ba ya da ilimi, ta inda shi mai hikima wanda yake da ilimi yake saurin cin moriya akan abubuwa saɓanin shi wanda yake da hikima amma ba ya da ilimi.
To amma ko ka san akwai bambanci tsakanin "hikima" da "manyance"? Akwai wanda suke son su ringa abubuwa na hikimomi amma sai su faɗa manyance ba tare da sun sani ba, musamman idan ba su yarda cewa ba su da ita (hikimar) ba, ta inda a lokaci guda manyancen kuma sai mutane su ɗauka hikima ce, kafin ka ankara kuma ya fara maida mutane shashashu "fooling" ɗinsu. Shikenan kuma ya zamo "shugaban sakarkaru" ba tare da su sun san ba hikima yake da shi ba zallan manyance ne kawai.
Sannan idan Allah ya yi ka mai hikima to haka za ka ringa abubuwan ilimi da azanci (koda ba ka je makarantar ba) amma kasancewar zamantakewa ko wata baiwa sai ka ga ya haska maka wasu abubuwan da masu ilimi kaɗai suke da ikon magana akai, wanin ma har ka fi su.
Shi mai hikima zai iya juya wani abu (idea) na mai ilimi ba tare da shi mai ilimin ma ya iya gane hakan ba. Akwai tarin misali dangane da haka.
Sannan kowane Ɗan Adam ba'a rasa shi da wata ɓoyayyiyar baiwa koda ba shi da ilimi, aƙalla yana da wata baiwar da Allah ya masa wadda ba kowa ya sani ba, wataƙila shi kansa ma bai lura yana da baiwar ba, ko kuma bai san hakan baiwa ba ce ba.