Sunday 3 November 2024

Dalilai 9 Da Ke Kawo Mikewar Azzakari Kaitsaye

Tura Wannan Zuwa Ga

 1. Priapism shi ne miƙewar azzakari na tsawon lokaci (tsawon awa huɗu zuwa shida [4-6 hours]) ba tare da sha'awah ba ko bayan sha'awan ya tafi, wanda hakan ya kan zo da tsananin zafi ga mai wannan matsalar. Mata sukan samu priapism na clitoris (clitoral priapism, clitorism), amma ɗaiɗaiku ne. 


Dalilan Da Ke Kawo Mikewar Azzakari Kaitsaye 
Hoto: Vice

2. Priapism ya kasu kashi uku kuma waɗannan rabe-rabe sun shafi yadda jini yake zuwa azzakari ne a yayin miƙewarsa wanda za mu yi magana akansa shi ne ischemic priapism kuma shi ne wanda ya fi faruwa a cikin dukkan priapisms (19 a cikin 20). Yana faruwa ne idan jini ya tsaya a cikin azzakari ya ƙi ya koma bayan tafiyar sha'awa ko kuma ya zo ya maƙale a cikin azzakari haka kawai ba tare da sha'awa ba. 


3. Babban abinda ke jawo wannan matsalar shi ne Sickle cell disease (cutar sikila). Sannan akwai magunguna da yawan shansu ke jawo 'ischemic priapism' kamar magungunan matsalar ƙwaƙwalwa (anti-psychotic drugs) wasu magungunan depression da ake ce musu Selective Serotonin re-uptake inhibitor (SSRI misali: fluoxetine, sertraline, paroxetine da sauransu). Yawan shan cocaine da cannabis (wiwi) yana jawo wannan matsalar. Yawan shan magungunan ƙarfin maza yana kawo wannan matsalar fiye da kowane magani. 


Akwai wata kunama da ake kira da Brazilian wander spider da kuma black widow spider, cizonsu yana kawo wannan matsala. 


4. Matsalar priapism matsala ce da ake buƙata a yi hanzarin garzayawa da marasa lafiya zuwa asibiti (emergency) da zarar an ga azzakari ya tsaya a miƙe fiye da awa huɗu (4 hours) tare da tsananin jin zafi. Abu na farko da likitoci suke yi shi ne ƙoƙarin kashe zafin wannan ciwo. Sannan sai a yi ƙoƙarin zuƙo jinin daga cikin azzakarin ta hanyar amfani da syringe. Idan hakan bai yi ba, za a yi amfani da syringe a tura ruwa mai tsafta (normal saline) cikin azzakarin don ya sauƙaƙa zuƙo jinin daga cikin azzakarin. 


5. Idan zuƙo jini bai yiwu ba, za a yi allurar phenylephrine a cikin azzakarin a ƙaramin dose, sai dai phenylephrine zai iya zuwa da side effects kamar matsalolin zuciya da sauransu. Ya zama dole a maida hankali kan wannan a yayin amfani da wannan magani. Yana da kyau mu fahimci cewa idan aka ce magani yana da side effect, hakan baya nufin tabbas side effects ɗin zai faru akan duk wanda aka yiwa amfani da maganin. Ana ambatawa ne don a kiyaye kuma a tsayar da maganin idan aka ga hakan ya faru, sai dai idan matsalar da maganin zai kawo bai kai matsalar da rashin amfani da shi zai kawo ba, kuma babu wani magani da ya fi shi rashin matsala. 


Za a iya amfani da allurar diethylstilbesterol (DES) ko terbutaline ga waɗanda suke yawan samun matsalar priapism. 


6. Idan magunguna suka ƙi, za a yi surgery. Surgery ɗin ya ƙunshi buɗe wani ɓangare na azzakari tare da buɗe hanyar da jini zai bar azzakarin. Surgery ya kan zo da matsalolin da zai iya sakawa mutum ya samu matsala a mazantakarsa (erectile dysfunction, impotence) amma akan kiyaye hakan ta hanyar penile prosthesis ko penile implant a lokacin da za a yi surgery ɗin. Wannan implant ɗin yana taimakawa wajen gujewa ƙanƙancewar azzakari bayan surgery. 


7. Ana magance priapism ga masu fama da cutar sikila ta hanyoyin da muka ambata a sama. Sai dai ana farawa da ƙara wa marasa lafiya ruwa (intravenous fluids), magance zafi ta hanyar amfani da magungunan kashe zafi masu ƙarfi da kuma taimakawa marasa lafiya wajen numfashi (oxygen therapy). Ana iya ƙara jini ta hanyar canza wa maras lafiya jinin da ke jikinsa (exchange transfusion) amma ba a son yin hakan sai ya zama dole saboda matsalolin da zai iya kawowa. 


8. Ga mai cutar sikila, babban abinda ya kamata a yi wajen rage faruwar priapism shi ne bayar da muhimmanci wajen rage cutar sikila, ta hanyar shan magungunan da suka dace da kuma kiyaye abubuwan dake ɗagawa ko tsananta ciwon. Za mu samu lokaci mu yi bayani daidai gwargwado akan cutar sikila (Sickle cell Disease [SCD]) in sha Allahu. 


9. Amfanin hydroxyurea ga mai cutar sikila ba shi da alaƙa da priapism. Ana bayar da hydroxyurea ne don yana taimakawa wajen ƙara yawan jini a jikin Ɗan Adam ta hanyar samar da sinadarai masu amfani wajen samuwar red blood cells kamar su Hemoglobin F da sauransu. Hakazalika yana rage yawan ruwan red blood cells, yana rage yawan neutrophils (wasu ɓangare ne na white blood cells), yana kuma taimakawa wajen kawar da cells ɗin da suke kawo matsala wa mai cutar sikila (sicked cells). Kamar yadda muka faɗa a baya, side effects baya nufin idan ka sha magani tabbas za ka samu side effect ɗin. Ana ambata maka ne saboda da zarar ka ga wannan matsala ka tsayar da shan magani ka garzaya wajen likita. Don haka muna ƙarfafa wa marasa lafiya su sha maganin nan kamar yadda likita ya faɗa musu. 


Idan yana buƙatar ƙarin bayani kan yadda ake shan maganin da kuma abubuwan da ya kamata a riƙa kiyayewa, sai ya tuntuɓe mu.


Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya.


Tushe/Asali:  Qaloon Health Support

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user