Sunday, 24 November 2024

Dalilan Samuwar Dabi'u Kyawawa Da Dabi'u Munana

Tura Wannan Zuwa Ga

A Falsafance ya nuna ƙiriƙiri dangane da alaƙar da ke tsakanin ƙwaƙwalwa (Brain) da ɗabi'a (Habit) wanda abubuwa guda biyu ne masu tafiya da juna hannu bibbiyu.


Dalilan Samuwar Ɗabi'u Kyawawa Da Ɗabi'u Munana
Hoto: R pics/Reddit

Marubuci:- Usman Yanmaza


Masana ilimin ƙwaƙwalwa wato "neurologists" suna nuni da cewa a cikin bangon ƙwaƙwalwa akwai wani gefe a cikin ƙwaƙwalwar wanda ake kira "Basal ganglia" wanda yake amfani wajen riƙon abubuwa wanda jiki ko ayyuka suke yi na yau da kullum, ita wannan Basal ganglia ɗin ita ce matattarar ɗabi'u koda a lokacin ƙwaƙwalwa tana bacci ko hutu.


A kan samu daga cikin mutane wanda suka samu rauni a Basal ganglia nasu za ka ga sun kasance suna da ciwon mantuwa wanda yanzu za ku yi magana amma cikin minti ɗaya ya manta, zai iya manta yadda yake wanka, zai iya manta fuskar abokansa da sauransu. A cikin dabbobi misali za ka ga ɓera yana da mantuwa, yanzu tarko zai kama shi amma ana cire shi zai sake komawa wajen tarkon saboda mantuwa.


Masanan sun ci-gaba da cewa "ɗabi'a" ta kan wanzu ne saboda "ƙwaƙwalwa" a kullum tana neman sauƙaƙa yadda za ta rage wahalhalu ga kanta ne, shi yasa take sarrafa aiki ko hankali da zuciya wajen bin jiki. Sannan ɗabi'a babbar aba ce a rayuwar Ɗan Adam, shin ka taɓa tambayar kanka me kake fara yi idan ka tashi daga bacci? Goge baki kake fara yi, ko banɗaki kake fara shiga, ko wanka kake fara yi? Sannan ka taɓa lura da abin da kake fara yi idan ka dawo daga wajen aiki ko wajen kasuwanci? Ka taɓa lura da abin da kake yi kafin ka kwanta bacci? Duk waɗannan suna daga cikin ɗabi'a wato "Habit management".


Amma abun tambayar anan shi ne ko ɗabi'a tana tafiya da ƙwaƙwalwa? Eh tabbas tana tafiya da ƙwaƙwalwa amma ba lallai ɗabi'ar ta zamanto mai kyau ba, ɗabi'a a muhallinta na "habit" tana da 'ya'ya wato ɗabi'u masu kyau "Good habits" da ɗabi'u marasa kyau "Bad habits". Amma fa kowanne daga cikin biyun sunan shi ɗabi'a.


Daga cikin Ɗabi'u Masu Kyau akwai wanda za ka ga masu shi kullum suna kyawawan abubuwa saboda ya bi jikinsu, misali kyauta, yawan gaisuwa, sabawa da jama'a, girmama mutane, taimako da sauransu.


Daga cikin Ɗabi'u Marasa Kyau akwai irin su shaye-shaye, rashin kunya, zagi, ta'addanci, sace-sace da sauransu.


Masana sukan faɗa cewa, kai za ka fara alƙalanci dangane da ɗabi'unka. Ka fi kowa sanin abubuwan da kake yi idan masu kyau ne ko akasin haka. 


Ƙwaƙwalwa abokiyar ɗabi'a ce na kyau ko akasin haka, matsalar shi ne sarrafa ƙwaƙwalwar wajen mai da ita ɗabi'a musamman masu kyau anan kuma jan aikin yake.


To ina mafita? Ku ci-gaba da bibiyar mu.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user