WANNAN BABBAN SAƘO NE NA MUSAMMAN GA ƊAN SHEKARA 40 DA WANDA KE DAF DA CIMMA SHEKARU 40.
Assalamu alaikum warahmatullah.
Ina fatan kun tashi lafiya, Allah Ya ƙara lafiya da sutura duniya da lahira.
Bayan haka, haƙiƙa rayuwa cikin musulunci da ƙoshin lafiya ni'imomi ne masu girma da babu abin da mutum zai yi sai dai ya yi ta godiya ga Allah Ta'ala a kansu tare da nuna gazawa da ƙasƙantar da kai a gare Shi.
Marubuci: Shehu Mansur Dala
Shekaru arba'in a duniya wani zango ne mai matuƙar muhimmanci a rayuwa wanda Allah Ta'ala ya nuna darajarsa domin a wannan lokaci ne Yake aiko manzanninsa masu girma. Kuma a wannan zango ne mutum yake zama kamili a kusan kowanne ɓangare na rayuwarsa, yake fara fahimtar haƙiƙanin rayuwa a bisa yadda take musamman idan ya samu kyakkyawar kulawa da ingantacciyar tarbiyya a baya.
Lokaci ne da tunani ya kan canja, abubuwa da yawa na salon rayuwa da jiki su sauya.
A lokacin farin gashi (furfura) yake kankama a kai da gemu, wasu ma tun kafin wannan lokacin ake ganinta.
Wani daga wannan lokaci alamun tsufa suke fara bayyana a gare shi, amma kuma a ilimance ba za a ce da ɗan shekara arba'in tsoho ba, amma yanayin rayuwa da tunani da cimaka na mutum shi ya kan sa ka ga yaro ya tafke, babba kuma ka gan shi kullum kamar yaro.
Waɗansu sukan firgice daga sun shiga shekara ta arba'in su ɗauka su tasu ta ƙare, mutuwa kawai suke jira musamman idan furfura ta yi gaggawar fesowa. Wannan kuskure ne domin idan shekaru 60 ko 70 aka yanka masa zai yi a duniya ai ka ga yana da sauran shekaru 20 ko 30 waɗanda zai iya yin abubuwa masu kyau da yawa a cikinsu.
Tsige furfura ko aske gemu don kada a ga furfurar mutum a ce ya tsufa haramun ne, ai haƙiƙanin tsoho shi ne wanda zuciyarsa da tunaninsa suka tsufa suka daskare, kuma ita furfura ado ce ga mumini kuma alama ce ta nutsuwa wacce take haifarwa da mutum kwarjini a idon mutane musamman idan an tsare mutunci.
Babu laifi a rina furfura da jar kala ko ruwan ɗorawa, amma a guji rina ta da baƙi.
CANZA SALON RAYUWA
Ya kamata ga ɗan shekara arba'in zuwa sama da ma wanda ya kusa kai wa arba'in ya canja salon rayuwarsa kamar haka:
ZUZZURFAR TUNANI
Mutum ya zaunar da kansa ya yi dogon tunani akan rayuwarsa ya gayawa kansa gaskiya ya tambayi kansa tambayoyi uku:
1 Shin me na aikata a shekaru arba'in da suka wuce? Waɗanne ire-iren nasarori na samu kuma waɗanne matsaloli na fuskanta a rayuwata?
2. Shin yanzu a wanne mataki nake na rayuwa, me nake yi?
3. Shin nan gaba me nake son yi? yaya kuma zan yi shi ?
TUNANIN ABUN DA ZA KA BARI
A yayin amsa tambaya ta uku ka yi tunani da aiki na gaske kan me za ka bari bayan mutuwarka wanda za'a riƙa tuna ka da shi ana yi maka addu'a saboda amfanarsa da mutane suke yi?
Wannan abu ne mai yiwuwa saboda mu dubi ɗimbin alkhairi da shugaban halitta ya bar mana mara yankewa wanda ya fara shi ne yana ɗan shekara arba'in. Ashe idan za mu yi koyi da shi ba za mu ce mun makara ba.
TUNANIN WA ZA KA BARI
Lallai a duk matakin da kake kai na rayuwa ka fara tattali da horon waɗanda za ka tafi ka bari domin ɗorawa daga inda ka tsaya a ayyukan alkhairi.
Idan kai Malami ne Malamai nawa za ka mutu ka bari a cikin ɗaliban ka waɗanda za su ci gaba da gwagwarmaya bayan mutuwar ka?
Idan kai Ɗan Kasuwa ne ko wani mai sana'a ko ma'aikaci, attajirai nawa ko ƙwararru nawa za ka tafi ka bari waɗanda da an gan su za a tuna ka a yi maka addu'a?
Kai har 'ya'yanka ka yi tunani kuma ka tsara ka kuma yi aiki don ganin wanne irin samari da 'yammata da iyaye za ka tafi ka bar wa al'ummarka? Wacce irin gudummawa za su bayar wajen ci gaban zuri'arka da al'umma gaba ɗaya?
CANZA GABA-ƊAYAN SALON RAYUWAR KA
Kusan kowanne ɓangare na salon rayuwar ɗan shekara arba'in zuwa sama da wanda ya kusa kai wa arba'in yana da buƙatar sake nazari da canjin salon gudanar da shi.
Waɗannan ɓangarori sun haɗa da:
1. CAJA BATIRIN IMANI
Ya kamata a ƙara yawaita ibadu masu ƙara imani da tausasa zuciya. Idan kuma ba a yi to a fara.
Misali ƙiyamullaili, farkawa cikin dare domin yin salla da addu'a, aƙalla awa ɗaya ko rabin awa kafin sallar asuba domin a ribaci wannan lokaci mai matukar fa'ida da albarka.
Yin azumin nafila koda sau uku ne a kowanne wata.
Yawaita aikin hajji da Umara ga wanda yake a kusa da garin Makka ban da na nesa. Jaddada tuba da yawaita istigfari.
2. IDAN AN GIRMA A SAN AN GIRMA
Ya kamata wanda ya kai wannan mataki na rayuwa ya san fa yanzu ya zama babba wataƙila an fara tara 'ya'ya, kuma manya sun fara tafiya nauyi ya fara yin yawa, to ya kamata a bar hululu a yi sallama da halaye marasa kyau musamman shaye-shaye, da taɓe-taɓe, da ɗauke-ɗauke da fitintinu da 'yan uwa da maƙota da abokai, a yi sulhu da kowa, a rungumi zumunci, a tallafawa 'yan uwa da sauran mabuƙata.
3. ME KA YI WA ADDININKA?
Ya kamata kowa ya yi wa kansa tambaya wacce irin gudummawa yake bayarwa ga addininsa? Kuma mai zai tafi ya bari na ci gaban addini bayan rasuwarsa?
Wani sai ya zo duniya ya koma bai yi wa addininsa wani abun a zo a gani ba, sai dai kawai ya tara kuɗi ya sayi ƙasa ya yi abubuwa kala-kala ya tafi, shi kenan. Lallai ya kamata a sake tunani, musamman waɗanda Allah Ta'ala Ya ba su dama ta dukiya ko ilimi ko muƙami.
Za ka iya shiga kwamitin wa'azi da musuluntar da waɗanda ba musulmi ba da sauransu.
KULA DA LAFIYA
Ginshiƙan samun lafiyar jiki da ƙarkonsa su ne:
1. Cin lafiyayyen abinci: A yawaita cin ganyayyaki da kayan marmari na asali ba na gwangwani ko kwalba ba. A rage cin jan nama. A guji shan taba sigari da giya da dukkan kayan maye. A tsara lokutan cin abinci. A rinƙa yawan shan tsaftataccen ruwa.
2. Samun wadataccen hutu: A ƙalla a kullum a samu barcin awa shida ba tare da yankewa ba, a wurin da iska take gewayawa. In da hali a haɗa da barcin rana koda na mintina 15 ne.
A gujewa tara barci a ka musamman saboda kawai ana kallo ko amfani da waya.
3. Kaucewa yawan ɓacin rai: Mutum ya guji duk abin da zai jawo masa fushi da ɓacin rai. Idan kuma abin ya faru a yi haƙuri, a kai zuciya nesa. A daina riƙo da hassada da gaba. Waɗannan halaye na saurin tsufar da mutum da haifar da cututtuka musamman na damuwa da karya garkuwar jiki. Yawan murmushi da farin ciki na inganta lafiya da samun tsawon rai a duniya.
4. Motsa jiki: Lallai a kullum mutum ya tabbatar yana motsa jikinsa musamman ta hanyar tafiya a ƙasa, aƙalla tsawon mintuna 40 a kullum.
GEMU BA YA HANA KARATU
A yanzu bayan ka girma za ka iya riskar abun da ba ka samu damar riska ba a baya na karatun addini da na zamani.
Za ka iya shiga harkar koyon karatun Alkur'ani da haddace shi, da kuma majalisai ko makarantun ilimi.
Akwai manyan Malamai da sai da suka girma suka fara neman ilimi kuma suka zama bijimai hamshaƙan malamai irinsu Ibn Hazmi da Izzuddin Ibn Abdussalam da Al-Imamai Alqaffal.
Haka kuma za ka iya komawa makaranta domin kammala karatun boko da yanayi ya dakatar da shi koda kuwa ta salon karatu daga nesa ne ko kuma buɗaɗɗun jami'o'i.
Ka sani cewa ƙwaƙwalwar ka tana da buƙatar abinci lafiyayye wanda shi ne ilimi.
Yi ƙoƙari aƙalla a kullum ka ware awa guda domin karatu, ba lallai sai littattafan larabci ba, akwai littafai na Hausa masu yawa da ɗimbin fa'ida.
ƘARA INGANTA ZAMAN IYALI
Anan ma ya kamata a ƙara nazari akan yanayin zaman da ake yi, a ƙara ƙarfafa hanyoyin zaman lafiya a toshe duk wata kafa ta fitina da tashin hankali.
A ƙara kulawa sosai da tarbiyyar 'ya'ya musamman manyan cikinsu. A riƙa ba su lokaci ana zama da su ana tattaunawa da su.
Idan da buƙatar ƙara aure a yi shi cikin fahimta, a yi adalci kuma a tabbatar za a iya yi ban da rigima.
Sha'awar jinsi ita ce ƙarshen abin da yake ƙarewa ga mutum. Wani ma sai ya tsufa sai sha'awar ta dawo kamar ta matashi (balagar tsufa) ya kamata ma'aurata da iyalansu su fahimci haka kada a zalunci kowa.
Waɗannan su ne muhimman saƙonni da masana suke isarwa ga 'yan shekara arba'in zuwa sama da waɗanda suke dab da shiga arba'in domin tattalin nasarori da aka samu da ƙara haɓaka su da kaucewa matsalolin da aka gamu da su a shekaru masu zuwa da kuma samun damar kyakkyawar cikawa da barin zuri'a managarciya.
Domin samun cikakken bayani duba:
✓جدد حياتك رسالة إلى من جاوز الأربعين للدكتور محمد موسى الشريف
✓صحتك بعد الاربعين المعصومة علامة
جدد حياتك لمحمد الغزالي
✓ريح النسرين فيمن بلغ الاربعين للشيخ محمد بلغوا بن عثمان بن فودي
Ina roƙon Allah Ta'ala Ya inganta rayuwar mu, Ya kyauta ƙarshenmu, Ya albarkaci zuri'armu, Ya tsare imaninmu gabaɗaya Amin.
Ku taimaka ku yaɗa wannan saƙon.
Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.
Maasallam.