Kada ki bar ni ina shawagi tamkar tsuntsu a sararin samaniya. Ƙaunar ki nake har can ƙarƙashin zuciyata.
Kalaman janyo hankalin sabuwar budurwa
Hoto: Dreams time
Marubuci:- Abba Rabi'u
Na tabbatar so yanayin shi ya kan sauya daga farin launi zuwa kore, son ki yana cikin zuciyata, amma ina kokwanton kada ya zama tsuntsu ya tashi, idan har ya kasance kin ci-gaba da nuna rashin kulawarki a kaina.
Kyakkyawa mai kyan tsari, a duk lokacin da nake kallonki, tamkar kyakkywar fulawa mai furanni ma'abota ɗebe kewa da sanya nishaɗi a zuciya ki kan zamo min.
Ki yi min agaji, ki tausaya min, ki tallafe ni, ki amince da ni a cikin zuciyarki, son ki ya gama shiga jikina.