Thursday, 7 November 2024

Gajerun Kalaman Soyayya A Rubuce

Tura Wannan Zuwa Ga

Abar alfaharina, ina sonki fiye da adadin lissafinki, adadin da zai iya zamowa tamkar zubar ruwan sama a lokacin damina. Ke kaɗai ce tawa.


Kalaman Soyayya A Rubuce
Hoto: Freepik

Marubuci:- Abba Rabi'u


Na zamo tamkar agwagwa, ina iyo a cikin kogin soyayyar ki.


Kyauta ta musamman a gare ki, ke kaɗai domin faranta ranki ya abar ƙaunata, baya  ga kaina da na ba ki, ga kuma kyautar furen soyayya.


Na kasance tamkar kifi a cikin ruwa, idan na yi gabas sai kuma na dawo na yi yamma, idan na yi kudu, sai kuma na dawo na yi arewa.


Da za ki tallafa, da kin kawo ƙarshen iyon da nake yi da ninƙaya domin gudun gazawar gwiwowina a lokacin da igiyar ruwa ta naɗe ni.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user