Da sunan Ubangijin da ya halicci zukatanmu a cikin jikin mu, ya ɗarsa ƙaunar junanmu ta yadda muka zama tamkar 'yan uwan juna saboda kamanceceniyar mu.
Gajerun Kalaman Soyayya Na An Wayi Gari Lafiya Ga Masoyiya
Hoto: Times of India
Marubuci:- Ridwan Khan Adam
Haƙiƙa na yi dace bisa yadda mutane kan tsinci kansu a wani hali a wannan lokaci amma ni yanzu sai sambarka domin na samu gwanata ga ta dab da ni.
Banda kowa ban da komai a zuciyata sai ƙaunarki.
Na wayi gari cikin masu aikin yi, wanda aikina shi ne rera baitocin ƙauna a gare ki.