Soyayyar ki tana ɗawainiya da rayuwata, ta gama ratsan zuciya. Ya abar sona ke kaɗai zan yi wa kwalliya, domin na san na dace da samun ɗiya mai tarbiyya, mai kyawun tafiya, ina ƙara tabbatar miki a duk sa'adda kika yi sassanyar dariyarki sai ƙaunarki ta ƙara ninkuwa a zuciyata.
Marubuci:- El-Nass
Masoyiya, ba na tunani, kuma ban taɓa kawo a raina cewa soyayyarki za ta taɓa gushewa daga zuciyata ba, kamar yadda na yi imanin falwaya ba za ta taɓa fitar da ganye ba, kamar yadda cewa ba za a taɓa samun jaki mai kaho ba.
Ina matuƙar girmama soyayya a rayuwata a saboda ke.
Duniyar soyayya wata duniya ce mai cike da farin ciki da sanya shauƙi a zukata, na shiga wannan duniyar ba na fatan fitowa daga cikinta, na san ma ba za ki taɓa bai wa wani ƙofar da zai shiga cikin ta ba balle ya takura mini har ya yi yunƙurin fito da ni.
So tamkar mikiya yake, yana ɗawainiya da zuciya, fatana na riski babban burina wato na mallakeki a matsayin mata a gare ni, uwar 'ya'yana mai tarairaya da ba ni farin cikin rayuwa.