Mai ƙin fitar da zakka iri biyu ne: Kodai ya ƙi bayarwa ne saboda bai yarda wajibi ba ce, ko kuma ya ƙi bayarwa ne saboda tsananin rowa da son abin duniya.
Idan ya ƙi bayarwa ne saboda bai yarda da wajibcinta ba, to ya kafirta. Idan kuwa don rowa ne, ko sakaci to fasiƙi ne. Kuma hukuma za ta iya karɓa ta ƙarfi daga gare shi.
Kamar yadda Khalifan Annabi (S.A.W), wato Abubakar (R.A) ya yaƙi waɗanda suka ƙi bayarwa a zamaninsa. (Duba Zakatul Ma’adni na Almukhtar bin Umar bin Al-Hussain As-Shankidi Sh:18-19).
Kuma ya kamata mu sani cewa, ƙin bayar da zakka yana sabbaba azaba mai muni ga mutum a lahira.
Ga dai hadisin da Muslim ya rawaito game da haka:
عن أبي هريرة قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: "ما من صاحب كنـز لا يؤدي زكاته إلا أحمى عليه في نار جنهم فيجعل صفائح فتكوى بها جنباه ووجهه حتى يحكم الله بين عباده في يوم كان مقدار خمسين ألف سنة. ثم يرى سبيله إما إلى الجنة وإما إلى النار. وما من صاحب إبل لا يؤدي زكاته إلا بطح لها بقاع قرقر. كأوفر ما كانت تستن عليه كلما مضى عليه أخراها ردت عليه أولاها، حتى يحكم الله بين عباده في يوم كان مقداره خمسين ألف سنة. ثم يرى سبيله إما إلى الجنة وإما إلى النار. وما من صاحب غنم لا يؤدي زكاتها إلا بطح لها بقاع قرقر كأوفر كانت فتطؤه بأظلافها وتنطحه بقرونها ليس فيها عقصاء ولا جلجاء. كلما مضى عليه آخرها ردت عليه أولاها حتى يحكم الله بين عباده في يوم كان مقداره خمسين ألف سنة مما تعدون. ثم يرى سبيله إما إلى الجنة وإما إلى النار...".
Fassara
Daga Abu Huraira (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, "Babu wani mai taskace kuɗi, wanda ba ya bayar da zakkarsa, face sai an ƙona shi (kuɗin) a wutar Jahannama ya yi faɗi sannan a dinga goga masa a gyaffansa da fuskarsa; har lokacin da Allah zai yi hukunci a tsakanin bayinsa, a yinin da yake kwatankwacin tsawon shekara dubu hamsin. Sannan a nuna masa hanyarsa, kodai zuwa aljanna ko kuma zuwa wuta.
Babu wani mai raƙuma wanda ba ya bayar da zakkarsu, face sai an jefa shi a cikinsu, a wani kwari mai faɗi, cikakkunsu. Sannan su dinga bi ta kansa. Idan suka kai ƙarshe, sai a dawo da na farkon, haka za a dinga yi masa, har Allah Ya yi hukunci a tsakanin bayinSa. A yinin da ya ke kwatankwacinsa tsawon shekara dubu hamsin. Sannan sai a nuna masa hanyarsa, kodai zuwa Aljanna ko zuwa wuta. Babu wani mai tumaki ko awaki wanda ba ya bayar da zakkarsu, face sai an jefa shi a cikinsu, a wani kwari mai faɗi, cikakkunsu. Sannan su dinga taka shi da kofatansu, suna sukansa da ƙahunnansu.
Babu mai tanƙwararren ƙaho a cikinsu, balle marar ƙahon. Idan suka kai ƙarshe, sai a dawo da na farkon, haka za a dinga yi musu, har Allah Ya yi hukunci a tsakanin bayinsa, a yinin da yake kwatankwacin tsawonsa shekara dubu hamsin. Sannan sai a nuna masa hanyarsa, kodai zuwa Aljanna ko zuwa Wuta…”. (Duba Nailul Audar na Shaukani, juz’i 2, sh:172-173).