Wednesday, 27 November 2024

Illar Da Zina Za Ta Yi Ga Rayuwar Matashi

Tura Wannan Zuwa Ga

Zuwa gare ka matashi: Zina ita ce tushen duk wani bala'i. Idan ka bijire wa dokokin Ubangiji, ba za ka taɓa samun albarkarSa ba a cikin al'amurranka.


Illar Da Zina Za Ta Yi Ga Rayuwar Matashi
Hoto: Gawrav/iStock photo

Idan ka kuskura ka aikata zina, to ka jefa kanka cikin wani tarko da ba ka da ranar fitowa daga cikinsa.


1. Za ta ɗaiɗaita rayuwarka, ta kassara mafarkanka/burinka, ta gusar da kwarjini daga fuskarka sannan ta tarwatsa alaƙar da ke tsakaninka da mutanen kirki.


2. Za ta zubar maka da mutunci hatta a idanunka, kai da kanka za ka bar ganin ƙima da mutuncin kanka, kuma hakan zai sa ka daina yin duk wani abu mai amfani ga rayuwarka. 


3. Za kuma ta haifar maka da shakku da tsoro da nadama a cikin ranka. Kullum kana ɗar-ɗar kamar wanda ya saci kaya yake tsoron a kama sa, saboda ka keta alfarman abin da Allah Ya tsarkake shi.


4. Za ka rasa ƙimar kanka da kaifin basira da azamarka sannan ka zama bawa ga sha'awarka. Tunaninka zai canza daga tunanin masu manufa zuwa tunani irin na dabbobi waɗanda ba su da aiki face ci da sha, da jima'i.


5. Ba a nan illar ta tsaya ba. Idan zina ta bi jikinka to ko ka yi aure ba za ka iya daina wa ba. Matarka ta halal ba za ta taɓa gamsar da kai ba, sannan za ka koma kallon duk wata mace da sha'awa wanda hakan zai sa rayuwarka ta tarwatse cikin gaggawa.


6. Kana tunanin za ka tsoma hannunka ne a cikin wuta ba tare da ta ƙona ka ba? 


Maganar gaskiya ita ce ba za ka taɓa tsira daga illolin wannan mugun aikin ba har abada. Don haka kada ka yi kuskuren afka wa zina, saboda illolin da za ta haifar ga rayuwarka ba su da iyaka. Duk a saboda gajeren sha'awa?


7. Zina ba wai zunubi ba ce kawai, amma kamar wata ƙofa ce da take shigar da mutum cikin wata rayuwa mai ɗauke da nau'o'in masifu da bala'o'i iri-iri.


8. Zina halaka ce kuma guba ce wacce za ta gurɓata zuciyarka da ruhinka, sannan ta wargaza rayuwarka. Za ta rugurguza iyalinka, da karatunka, da kasuwancinka, da sana'arka sannan ta raba ka da komai.


9. Za ta lalata alaƙarka da Mahaliccinka sannan ta bijirar da kai ga haɗurran shaiɗan da kuma haɗurran zuciyarka. 


Za ta cire maka nutsuwa a zuciyarka, kuma ko kana da dukkan abin da kake so ba za ka samu kwanciyar hankali ba.


10. Ka nemi aure, kuma ka fifita kamewa akan sha'awa na ɗan ƙaramin lokaci wacce za ta halakar da kai.


Aure yana da tsarki kuma yana da alfarma. Alƙawari ne wanda Allah da kanSa Ya zama shaida a ciki. Amma idan ka afka wa zina, babu kai babu tsarki, ko kariya da kiyayewar Ubangiji.


Daga nan za ka fuskanci duk rigingimun rayuwa a karan kanka. Babu kai babu jagorancin Ubangiji. Allah Ubangiji Ya mana kariya.


Duk abin da ba wannan ba kuwa tafarki ne da zai kai ka ga halaka da taɓewa!


Tushe/Asali: Hausa Motivation

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user