Monday, 4 November 2024

Illolin Yi Wa Mace Ƙarya A Soyayya

Tura Wannan Zuwa Ga

Abin da maza suka kasa fahimta ita mace tana ɗabi'antuwa ne da yadda ka ɗabi'ance ta, kuma tana yanke shawara ne ko kuma ta ɗoraka mizani da abin da ka gaya mata.


Illolin Yi Wa Mace Ƙarya A Soyayya
Hoto: Every pixel

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Ba wani alfanu don kuna soyayya da mace ka yi ta ƙoƙarin burgeta ta fannin sanya suturu masu tsada, da riƙe waya mai tsada da takurawa kanka ɗaukar wata hidimar ta wadda ba ta zama dole ba.


Shiyasa wani auren tun kafin a ɗaura shi ake ɗauko hanyoyin karya shi, namiji na jan ra'ayin mace ne da zantuttukan da yake mata sai kuma yadda ya ɗabi'ance ta. Idan ya kasance kana samun mace tun kafin ku yi aure kana gabza mata ƙarya kana gaya mata abin da ka san ba za ka iya ba ko kuma kana mata buƙatun da sun fi ƙarfin samunka. To lallai ko kun yi aure za ku fuskanci matsaloli gagarumai/sosai.


Saboda da ma ta aure ka ne saboda labarin wannan rayuwa da ka ba ta za ku gudanar idan kun yi aure. Kuma ta zo ta ga ba haka ba ko kuma ka kasa aiwatar da abin da ka gaya mata za ka dinga mata idan kun yi aure.


Kada ka ɗauka mata kamar maza suke, mace duk abin da ka gaya mata wallahi tana sane, abin da kake ganin bai kai ya kawo ba, yana nan a ransu. Kuma idan zance ya kama wataran sai sun tuna maka rana kaza ka ce abu kaza.


Don haka ka koyi cewa mace "A'a" a kan abin da ka san ba za ka iya ba, ko kuma ba ka da tabbas ɗin za ka yi ko ba za ka yi ba, hakan zai sa ka auri wadda ra'ayinku yake ɗaya ko kuma za ta iya zama da kai a yadda kake.


Amma ka ga ƙato ya gwaggwafe ya ji daɗin ƙamshin turaren yarinya da ta fesa yana ta zabga mata zantuttukan da kana ji ka san ƙarya ne.


Kamar irin su:


"Baby tare za mu dinga wanke-wanke da shara.".


"Baby ni zan dinga raka ki awon cikin ɗan da za ki haifa min mai suna Ibn Qudama.".


"Baby gidan da nake gina mana hawa uku ne.".


"Baby ba za'a dinga girka tuwo a gidana ba.".


Malam wane ne ya tambayeka?


Waɗannan ƙananun maganganun da kake rainawa wanda ni da kai mun san duk ba za ka iya ba, su za su zame maka matsala. Ita mace tana riƙe da su a ranta kuma ba mamaki ka ja ra'ayinta ne da su dalilin haka ta yi watsi da sauran samarinta ta aure ka. Yaya kake gani idan ta zo ta ga ba haka ba?


Ka koyi cewa mace A'a.


Ka zauna lafiya.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user