A rayuwa komai za ka yi da akwai ƙalubale wannan shi ne abu na farko da ya kamata ka sani kafin ka tunkari duk wani abu da ka ke son cimma a rayuwa.
Marubuci:- Ibraheem Aleeyu
Sau da yawa mutum zai durfafi wani abu da ƙwarin gwiwar cin nasara, iya bakin ƙoƙari yana yin duk wani abu da zai kai shi ga cimma nasara, har ma ya zamana cewa ya fara gano alamun nasara a wannan tafiyar tashi, ya kan tsinci kansa a cikin matuƙar nishaɗi a duk lokacin da ya tuna cewa yana cin nasara, inda wannan nasara da ya ke samu take ƙara ƙarfafa masa gwiwa.
Kwatsam! Sai wani abu ya faru da duk wannan doguwar tafiyar da ya ɗauki dogon lokaci yana yi ta dawo baya, har ma ya zamana cewa ya dawo inda ya fara ko ma ƙasa da haka, to shin me zai faru a wannan lokacin?
Ko kuma a'a ba wannan ba, ya fara tafiyar zuwa ga cikar muradun sa sai dai tun a matakan farko matsaloli suka yi ta faruwa har ya kasa wucewa zuwa matakin gaba, shin me zai faru?
Sau da yawa dai mutane kan sare, ya zamana cewa duk wannan ƙoƙarin da suka ɗauki dogon lokaci suna yi ya zama a banza, ya zamana cewa duk tarin darussan da ke tattare da wannan ƙalubalen da suka fuskanta ya zama a banza, ba ma iya wannan ne matsalar ba, sai ya tsangwami kansa ya shiga cikin matuƙar damuwa, har ma ya cutar da kansa, ya zamana cewa babu wani amfani a fara wannan tafiyar tashi.
Nasara gaba ɗayan ta cikar buri ce, hakazalika shi cikar buri wani abu ne da ba ruwansa daga inda kake? Wane ne kai? Abin da kawai ya shafa shi ne inda ka sa gaba. Wannan kuma wani abu ne da kowa ya ke tsarawa kansa shi.
Abu na farko dai wannan ƙalubalen da kowa ke fuskanta a rayuwa, zai iya kasancewa kala biyu:
1. Kodai ya kasance laifinsa ne ma'ana ya yi wani kuskure da hakan ya zama sanadiyar samun wannan matsalar, ta yiwu bai yi kyakkyawan tsarin da zai taimaka masa wajen cimma nasara ba, ta yiwu shi da kansa bai tsara ina?, Ta ya? Yaushe zai kai ga cimma nasara ba, ko kuma duk ya yi kyawawan tsare-tsaren da zai kai shi ga nasara amma ya kuskure hanya, To anan me ya kamata ya yi?
2. Sai kuma ƙaddara: Wannan kuma Allah ne ya ƙaddara, kwatsam kana tara kuɗi domin samun jari sai aka sace, kwatsam ka buɗe shagonka sai aka yi gobara, kwatsam ka yi nisa a tafiyar cimma nasarar ka sai wani abu da ba makawa sai ya faru bisa ƙaddarar Allah ya faru ya dawo da doguwar tafiyarka zuwa inda ka fara, shin me ya kamata ka yi?
A ɓangare na farko, da na biyun duka mutane da yawa suna kauce hanya har ya zamana wasu sukan rasa imanin su ba tare da sun sani ba, abu ne da kowa ya sani cewa rayuwa cike ta ke da ƙalubale, kuma kowa da ka gani komai nisan da ya yi a tafiyarsa ta samun nasara za ka samu cewa kafin ya kai ya fuskanci ƙalubale masu ɗumbin yawa wata ƙila fiye da kai, hakazalika a mabambanta wurare a cikin Kur'ani, Allah subhanahu wata'ala ya ce "Tabbas ya zama lallai a jarrabi mutane". Ma'ana dai rayuwa cike take da ƙalubale ba za kuma a taɓa cin nasara ba, sai an faɗi, wani mai hikima ya ce "Faɗuwa rabin nasara ce.".
Bisa ga haka, abin da ya kamata shi ne a duk lokacin da ka faɗi, ka dawo tushen tafiyar ka, to ka binciko kurakuranka, ka yi ƙoƙarin fahimtar su da kuma ɗaukar aniyar gyarawa, ka sanyawa kanka ƙwarin gwiwa fiye da lokacin da ka fara, kada ka sake ka ce bari na jira wani lokaci na ƙara gwadawa. Wannan zai iya zama wani abu da zai mantar da kai kurakuranka na baya koda a ce ka ƙara gwadawa, da rashin ma bincike kurakuran naka, sai ya zamana cewa wannan tafiyar taka ta farko ma ba ta yi maka amfanin komai ba, ka sake tsunduma wata tun kafin ka fara tafiyar, abinda ya kamata ka fara shi ne sanin cewa za fa ka iya ƙin yin nasara, to me za ka yi bayan hakan?
Ƙaddara
Idan kuma ƙaddara ta afka maka, kada ka yi baƙin ciki, kada ka damu kanka ka hana kanka walwala tare da tunanin cewa shikenan ba za ka iya cika burin ka ba, shin ba ka san cewa Allah ya ce "Shin mutane na zaton cewa za'a bar su kawai don sun ce sun yi imani ba tare da an jarrabe su ba/fitine su ba". Ko kuwa da ma kana zaton cewa za ka ci nasara ne a hanya simbiɗal/sambel ba tare da tuntuɓe ba? A cikin littafin The Seven Habits of Highly Effective Peoples ya cika littafin da bayanin ci-gaba da gwagwarmaya bayan faɗuwa na ɗaya daga cikin halayen waɗanda suka ci nasara.
Mafita
Abu na farko, kada ka damu kanka, yadda ka fara tafiyar kada ka sake ka dakata, ci-gaba da tunkara tare da gyara kurakuran da ka yi a tafiyar ka ta baya, ka dinga ji a ranka cewa wannan abin da ya faru da kai Allah subhanahu wata'ala yana da wani shiri na musamman gare ka da ya fi naka, kada ka sake ka sare koda za ka dinga dawowa farkon tafiyarka sau dubu, har sai idan ka kai ga cimma burin ka, kuma ka tabbatar da cewa cikar wannan burin naka amfanin rayuwar ka ne, ba wai shirme ba.
Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.