Saturday, 23 November 2024

Ire-iren Zawarawa A Ƙasar Hausa

Tura Wannan Zuwa Ga

Na fahimci cewa zawarawa kala uku ne saboda yadda na tattauna da su.


Ga su kamar haka:


1. Akwai tsaka-tsaki tana son auren kuma ba ta son ta yi, saboda tana tsoron kar ta auri wanda bai kai mijinta ba ko wanda ba zai iya riƙeta ba, ko kuma tsoron inda ta baro a sake maimaita koma mene da ta baro ko kuma tana son ta yi auren saboda tana da imanin za ta iya samun sauyin rayuwar da ta baro ko za ta iya samun kamar mijinta ko wanda ya fi shi ma, su ma irinsu sukan ɗan jima saboda fargaba da kuma son yin auren da suka haɗu suka taru a zuciyarsu.


Ire-iren Zawarawa A Ƙasar Hausa
Hoto: USA Today

MarubuciyaFatima Zahra


2. Akwai wacce idan kana son ta daina maka magana to ka ce mata "Ya kamata ki yi aure". Idan tana ganin mutuncinka ne za ta ɗan yi murmushi ta ce "Lokaci ne!". Saboda ta sha wuya, duk nazarinta hakan take ko'ina, sai ta saka wani abu a gaba wanda take ganin shi ne nutsuwarta a tunaninta.


3. Akwai wacce kuma take son yin auren Allah bai kawo mijin ba, saboda nata ya rasu ko kuma an kyautata mata amma ba ta gani ba, ta sa aka sake ta saboda halinta.


Shawara


Idan laifinki ne, ki nemi yafiyar wanda kika yi wa laifi, don aure ya fi komai bin haƙƙi, idan ya yafe shikenan. Idan ya rasu ne, ki yi haƙuri ki yi masa addu'a, ki yawaita neman zaɓin Allah, ki manta da komai. 


Na san da ciwo, wata za ta ce "Sai na ji tamkar mijin yana kallona". Idan kuma rashin kwanciyar hankali ne, ki sani Allah yana iya canja miki da abin da ya fi alkhairi.


Ke dai ki kama mutuncin kanki a duk inda kike, ki kama Allah, yana taimakon wanda yake tare da shi.


Ya Allah ka aurar da 'yammatanmu da zawarawanmu ga mazaje masu adalci, ka sanya su su zamo mata nagari a gare su Amin.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user