A duk lokacin da na buɗe idanuwana babu wanda nake fara gani sai kai Habib, na je makaranta amma na kasa zama saboda tsananin tunaninka da ya shige mini zuciya Habib.
Marubuci:- Rabs
Burina ba zai kammala cika ba har sai na tabbatar mizanin soyayyata da taka sun yi kunnan doki kuma ba zan taɓa gazawa ba Habib har sai burina ya cika.
Me kake so na dafa maka ka ci yanzu kawai a matsayin kyauta?
Na gode maka da ka kasance a cikin rayuwata saboda ba ni da wani buri face na samu abokin rayuwa kuma na samu, sannan zan ci gaba da ƙoƙarin ganin na ci-gaba da rura wutar soyayyata a cikin zuciyarka.
Tabbas ire-iren waɗannan kalamai su suke zautar da mutum a yayinda budurwasa take sambaɗo masa su har ya zauce ya dinga kiran wayyo duniyata.
Da fatan 'yammatan wannan shafi za ku ƙara dagewa wajen kulawa da masoyanku ta hanyar faranta musu zuciya?