Friday, 15 November 2024

Kalaman Soyayya Cikin Hikima

Tura Wannan Zuwa Ga

Zuwa ga kamilalliyar mace mai kyau da tsarin siffa. Ke ce sarauniyar da ke mulkin birnin zuciyata, ke ce farin wata mai haske mini zuciya, ke ce abar sona, ke ce ganina, kuma ke ce jinina.


Kalaman Soyayya Cikin Hikima
Hoto: Alasd Aljmyl

Marubuci:- Ridwan Khan Adam


Zan kasance tare da ke a duk inda kike, cikin mafarkinki, cikin tunaninki, cikin farin ciki da baƙin ciki.


Fatana ki kasance cikin farin ciki da annashuwa, fatana ki zamto tauraruwar da ke haske duniyar mutane.


Zan kasance mai share miki hawayenki, ya ma za'ai na bar idanuwanki su zubar da hawaye? Komai na jikin ki yana da muhimmanci a gare ni.


Ba na son ganin kowa sai ke kaɗai, ba na son jin muryar kowa sai taki kawai, son ki ya zame mini abokin hirata.


Na kan kasance cikin farin ciki a duk lokacin da na yi arba da fararen idanuwan ki. Ke ce tawa har abada, ki huta lafiya.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user