Wednesday, 27 November 2024

Kalaman Zolaya Da Wasa Da Hankalin Masoyi

Tura Wannan Zuwa Ga

Kashi uku cikin huɗun zuciyata ne kawai zan ba ka, cikon na huɗun ba zan bada ba. 


Ta iya yiwuwa duka kaso uku cikin huɗun da na ba ka su ɓata, ka ga kenan zan ci ribar kaso ɗayan da ya ragu.


Kalaman Zolaya Da Wasa Da Hankalin Masoyi
Hoto: Voyagerix/Dreams time

MarubuciTaska


Yo wai kai dama burinka shi ne na mutu idan tarayyar mu ta watse?!! 


To ya kenan? 


Yo kai ka yarda ne? 


Kai! 


Da gaske!?


Kai ni fa wasa nake maka, zuciyata gaba ɗaya taka ce, koda zan mutun, to na yarda cewa ina matuƙar ƙaunarka!


To wa ya sani cewa ta iya yiwuwa idan na kawo maka ziyara, kawai sai ya zamana ka canza min fuska?


Har ka ci gaba da nuna jayayya da taurin kai da jiji da kai, kana mai gwada min ƙwanji.


Kai ta iya yiwuwa ma gobe-goben nan na koka da kai, a maimakon na yi bayani da Hausa.


Kowa ya fahimce ni, sai ya zamana kamar ma Turanci ko Turkanci nake yi, babu mai fahimtata.


Haka nan zan ci-gaba da ƙoƙarin yin kukan zuci mara hawaye.


To ya kenan?


Yo kai ka yarda ne? 


Kai! 


Da gaske!?


Kai ni fa wasa nake maka, zuciyata gaba ɗaya taka ce, koda zan mutun ɗin, to na yarda cewa ina matuƙar ƙaunarka!


Kashi uku cikin huɗun zuciyata ne kawai zan ba ka, cikon na huɗun ba zan bada ba.


Ta iya yiwuwa duka kaso uku cikin hudun da na ba ka su ɓata, ka ga kenan zan ci ribar kaso ɗayan da ya ragu.


To wai kai da ma burinka shi ne na mutu idan tarayyar mu ta watse ?


To ya kenan? 


Yo kai ka yarda ne? 


Kai! 


Da gaske!?


Kai ni fa wasa nake maka, zuciyata gabaɗaya taka ce, koda zan mutun, to na yarda cewa ina matuƙar ƙaunarka!


Yo wai ma wane ne ya san ƙaddarar da zai iya faruwa, ta iya yiwuwa fa na wayi gari na yi asarar soyayyarka.


Kai idan har kana kwaɗayin na yi maka fiye da haka ne, kawai tun yanzu kowa ya kama gabansa.


Ta iya yiwuwa fa goben nan ka kamu da son wata, nan take ka manta da ni, zuciyata ta koma tamkar wani shaho ne a sama, ina ɗaga kai ina kallon sa.


To ya kenan? 


Yo kai ka yarda ne? 


Kai! 


Da gaske!?


Kai ni fa wasa nake maka, zuciyata gabaɗaya taka ce, koda zan mutun, to na yarda cewa ina matuƙar ƙaunarka!


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user