Muhammad M. Zakir Niger wanda aka fi sani da M. Zakir Niger ɗaya ne daga matasan mawaƙa na Kannywood masu tasowa a halin yanzu.
Hotunan sun ɗauki hankula sosai a shafukan Sada Zumunta duba da yanayin yadda aka ɗauki hotunan, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa sosai wajen ƙayatar da al'umma daga sassa daban-daban na faɗin duniya.
Waƙar Daram da waƙar Daga Allah da waƙar Ƙaddarata da waƙar Na Sani da waƙar Ba Zama, duk suna daga cikin fitattun waƙoƙin sa waɗanda su zama silar karɓuwar shi a gurin samari da 'yammata.
Yanzu haka dai akwai sababbin waƙoƙin sa da ya saki masu suna Kalar Dawisu/Dawisu da Ba Damuwa.
Waɗannan wasu ne daga cikin kyawawan hotunan nasa.
Ƙalli ƙarin wasu hotunan a ƙasa:
M. Zakir Niger Mawaƙi ne kuma Makaɗi ne, sannan kuma ɗaya ne daga cikin mawaƙan ƙasar Niger masu tasowa.
Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe domin samun ainihin cikakken tarihin M. Zakir Niger nan bada dadewa ba tare da zafafan hotunan shi na musamman.