Sunansa
Cikakken sunan sahabi Abubakar shi ne, Abdullahi ɗan Usmanu ɗan Amiru ɗan Amru ɗan Ka'abu ɗan Sa'adu ɗan Taimu ɗan Murratu. Zumuncinsa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya haɗu ne a kakansa na shida "Murratu" wanda shi ma kaka ne na shida ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
Marubuci: Saliadeen Sicey
Ana yi masa laƙabi da "Atiƙu", ana kuma kiransa Abubakar, sannan ya shahara da "Siddiƙu", sunan da ya samu bayan da ya gaskata Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin da mutane ke ƙaryata shi.
Mahaifansa
Sunan babansa Usman. Ana kuma yi masa alkunya da Abu Ƙuhafa. Mahaifiyarsa sunanta Ummul Khair, Salmah ɗiyar Sakhr ita ma daga ƙabila ɗaya ta fito da babansa, wato ƙabilar Banu Taim wadda ƙaramar ƙabila ce ƙwarai idan aka kwatanta ta da irin Banu Abdi Manaf da Banu Makhzum da sauransu.
Haifuwarsa
An haife shi a garin Makka a shekara ta hamsin da ɗaya kafin Hijira. Don haka Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya girme shi da shekara biyu da watanni kaɗan.
Siffofinsa
Abubakar mutum ne fari, siriri, mai zurfin ido, da babban goshi. Ga shi kuma ya ɗan sunkuya kaɗan. Saboda sirirantakarsa, wando ba ya ɗauruwa da kyau a ƙugunsa.
Ɗabi'unsa da Halayensa
Abubakar Raliyallahu Anhu ya kasance ɗaya daga cikin fitattun 'yan kasuwa masu fatauci. An bayyana shi da halin kirki da kyauta. Ƙuraishawa na darajanta shi saboda dattakunsa da karamcinsa.
Yana daga cikin abin da ke bayyana kaifin hankalinsa, haramta wa kansa shan giya da ya yi shi da abokinsa Usman ɗan Affan. Ba wanda ya taɓa kurɓa ta daga cikinsu tun kafin bayyanar Musulunci.
An ba da labarin cewa, tun asali Abubakar ya haramta wa kansa shan giya ne saboda ya ga wani mutum da ya bugu da ita yana sanya hannunsa a cikin najasa ya kuma nufi bakinsa, kana idan ya ji wari sai ya janye hannunsa daga bakin. Daga nan ne Abubakar ya ƙyamace ta har ya yi rantsuwa ba zai sha ta ba.
Haka ma bai taɓa bautar gumaka ba domin da Allah ya nufi kawar da shi daga wannan sai mahaifinsa ya je da shi yana yaro ya kai shi a wurin gumaka ya sanar da shi cewa, ga iyayengijinsa nan waɗanda ake bauta, ya tafi ya bar shi a nan. Shi kuma Abubakar da ya ji yunwa sai ya roƙe su abinci bai ji sun ce masa uffan ba, ya roƙe su ruwa ba su ce masa ci kanka ba. Daga nan ya tofa ma su yawu, ya zage su, ya tafiyarsa yana mai tsananin ƙyamarsu da ƙaurace masu.
Haka ma Abubakar bai iya waƙa ba. Ba za mu yi mamakin waɗannan ɗabi'un na Siddiƙu ba sanin cewa, shi babban aboki ne, masoyi ga shugabanmu Sallallahu Alaihi Wasallama tun zamanin ƙuruciya har manyanci. Mutum na kirki kuwa daga abokanshi ake ganewa.
Iyalinsa
Abubakar Raliyallahu Anhu ya auri mata biyu kafin Musulunci, biyu bayan Musulunci. Matansa na farko sun haɗa da:
1. Ƙutailah ɗiyar Abdul Uzzah, wadda ta haifa masa Abdullahi da Asma'u.
2. Ummu Ruman ɗiyar Amir ‘yar ƙabilar Kinanata, wadda ta haifa masa Abdul Rahman da Uwar Muminai A'ishah.
Matansa na daga bisani kuwa sun haɗa da:
1. Asma'u Ɗiyar Umais, wadda ta fara auren Ja'afar Ɗan Abu Ɗalib. A bayan rasuwar Abubakar kuma ta auri Ali Ɗan Abu Ɗalib. A kowane gida daga gidajen uku da ta yi aure ta haifi Muhammad. A wurin Ali kuma ta haifi Yahya da Aunu kamar yadda za mu gani a nan gaba.
2. Habibah ɗiyar Kharijah daga cikin Ansaru (Mutanen Madina), Ya rasu ya bar ta da cikin 'yar autarsa Ummu Kulsum.
Matsayinsa kafin zuwan Musulunci
Abubakar ya yi fice a zamanin jahiliyya da ilmin da ake kira Ansab, sanin dangantakar mutane da tarihin gidajensu da abubuwan arziki ko rashin arzikin da suka gudana a tsakanin mutane ko a tsakanin ƙabilu. Sannan kuma shi ne wakilin reshen gidansu a majalisar zartastawa ta ƙuraishawa wadda ta haɗa rassa goma na wannan ƙabilar, kowane gida yana da aikinsa da wanda yake wakilatarsa.
Ga su kamar haka:
1. Banu Hashim: Su ke kula da shayar da alhazzai ruwa. Wakilinsu a Majlisa shi ne Abbas ɗan Abdul Muɗɗalib, baffan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Wannan ofis nasu ya ci gaba da aiki bayan zuwan Musulunci.
2. Banu Umayyah: Su ke riƙe da tutar ƙuraishawa, kuma su ke riƙon ƙwarya duk lokacin da aka rasa shugaba kafin a haɗu a kan sabon da za a naɗa. Wakilinsu a Majlisa shi ne Abu Sufyan ɗan Harb.
3. Banu Naufal: Su ke kula da asusun tallafi na taimakon alhazan da guzuri ya yanke musu. Wakilinsu shi ne Al Haris ɗan Amir.
4. Banu Abdid Dar: Su ke kula da wanke Ka'aba da tufatar da ita. Wakilinsu shi ne Usman ɗan Ɗalha.
5. Banu Asad: Su ke da ofishin Sakatariya. Duk shawarar da aka yanke su ke sa mata hannu kafin a aiwatar da ita. Wakilinsu shi ne Yazid ɗan Zam'ah ɗan Aswad.
6. Banu Taim: Su ke da alhakin haɗa kuɗi don biyan diyya idan aka sasanta masu faɗa da kuma biyan bashi idan wani baƙuraishe ya kasa. Wakilinsu shi ne Abubakar ɗan Abu Ƙuhafa.
7. Banu Makhzum: Su ke kula da wurin ajiyar kayan yaƙi. Wakilinsu shi ne Khalid ɗan Walid.
8. Banu Adiyyin: Su ne masu kula da hulɗar ƙuraishawa da sauran ƙabilu, musamman a wajen sha'anin yaƙi da zaman lafiya. Kuma su ke da alhakin shelanta darajojin ƙabilarsu don ta yi kwarjini a idon sauran mutane. Wakilinsu shi ne Umar ɗan Khattab.
9. Banu Jumah: Su ke kula da ƙuri’ar da ake yi don neman sa'a in za a yi tafiya ko ciniki ko aure ko makamancinsu. Wakilinsu shi ne Safwan ɗan Umayyah.
10. Banu Sahm: Su ke kula da tattalin arziki da abinda ya shafi gumaka. Wakilinsu shi ne Al Haris ɗan Ƙais.
Musuluntarsa
Masana tarihi sun ruwaito cewa, tun kafin wahayi ya fara sauka ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Abubakar ya yi wani mafarki wanda ya labarta shi ga babban malamin nan masanin addinin Nasara da ake ce ma Bahirah. Sai ya tambaye shi daga ina ka fito? Ya ce masa daga Makka. Ya ce, kai wane iri ne? Ya ce masa, Baƙuraishe. Ya ce, mene ne sana'arka? Ya ce, Fatauci. Bahira ya ce, idan Allah ya gaskata mafarkinka to, wani Manzo zai bayyana daga cikin jama'arka, za ka taimaka masa a rayuwarsa, kuma ka wakilce shi bayan mutuwarsa.
A wata tafiya kuma da ya yi zuwa ƙasar Yaman ya samu bushara mai kama da wannan daga wurin wani malami daga ƙabilar Azd.
A lokacin da Allah Maɗaukakin Sarki ya aiko Manzonsa, Abubakar bai yi wata wata ba ya gaskata shi yana mai cewa, ba mu taɓa gwada ƙarya a kanka ba, kuma ka cancanci manzanci saboda tsaron amanarka da sada zumuncinka da kyakkyawar zamantakewarka da jama'a. Daga nan kuma Abubakar ya ci gaba da zama na hannun daman Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama har in da mai raba masoya ta raba su.
Gudunmawarsa ga Addini
Kasancewarsa mutum mai arziki, dattijo, kuma na hannun daman Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba shi damar taimaka ma addinin Musulunci ta hanyoyi da dama; A Makka ya kasance mai bada kariya ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama daga musgunawa da cin zarafin da mushrikai su ke masa. Har ma Ali Ɗan Abu Ɗalib (R.A) yake cewa, bayan mutuwar Abu Ɗalib babu wanda yake ce wa kafirai tinƙanzil idan suna musguna ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai Abubakar. Ga kuma dukiyarsa da ya yi amfani da ita wajen ci gaban addini har ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da kansa yake cewa, "Dukiyar kowa ba ta amfane ni ba kamar yadda dukiyar Abubakar ta amfane ni".
Abubakar ya taya Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wajen kiran mutane zuwa ga Musulunci inda ya janyo musuluntar kusan dukkan muƙarrabansa da amintattunsa kamar su Usmanu ɗan Affan da Zubairu ɗan Awwam da Ɗalhatu ɗan Ubaidullah da Abdur Rahman ɗan Aufu da Sa'adu ɗan Abu Waƙƙas waɗanda dukkansu suna cikin mutane goma da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa bushara da aljanna. Sannan daga bisani ya musuluntar da Usmanu ɗan Maz'un da Amiru (Abu Ubaidah) ɗan Jarrah da Arƙamu ɗan Abul Arƙam da Abu Salamata al Makhzumi waɗanda su ne magabatan farko a shiga Musulunci.
Abubakar ya gina wani ƙaramin Masallaci a farfajiyar gidansa da ke Makka inda yake Sallah da karatun Alƙur'ani. Ga shi kuwa mutum mai daɗin sauti da laushin murya wadda yake garwaya ta da kukan tsoron Allah, abinda ya sa da dama daga talakawan Makka suka rinƙa zuwa saurarensa, wasunsu kuma a dalilin haka suka musulunta. Kuma duk barazanar da mush'rikai su ka yi masa a kan wannan ba ta sa ya daina ba.
A lokacin da yawan musulmi ya kai mutum tamanin da uku sai Abubakar ya nemi manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da su fito fili su yi kira zuwa ga gaskiya. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya lurar da shi irin haɗarin da ke tattare da ɗaukar wannan mataki a daidai wannan lokaci, amma Abubakar ya nace akan cewa sai su gwada sa’arsu. Hakan ko aka yi. To, amma fa ba wanda ya biya harajin wannan kasada sai shi Abubakar ɗin. Domin kuwa fitowar su ke da wuya, da suka isa masallaci sai Abubakar ya tashi don ya gabatar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama zuwa ga mutane.
Ai kuwa ba su bari ya rufe bakinsa ba sai suka fara yi wa musulmi a ture cikin masallaci mai alfarma. Nan take kuwa suka tarwatsa taron musulmi. Sannan suka far ma Abubakar da duka har sai da suka kai shi ƙasa. Sannan Utbatu ɗan Rabi’ata ya ɗare akan cikinsa yana amfani da takalma wajen dukan fuskarsa. Bai gushe ba yana yi masa duka har sai da hankalinsa ya gushe, fuskarsa ta yi jinajina har ba a iya bambanta hancinsa da bakinsa.
Ƙabilar Abubakar ta Banu Taimin sun yo ciri don su ceci ɗan uwansu. Amma koda suka zo gayya ta gama aiki, mush'rikai sun yi ta’adin da suke so akan Abubakar. Suka ɗauke shi a halin suma suna tsammanin ya mutu suka kuma lashi takobin idan ya mutu za su kashe Utbatu ɗan Rabi’ata abinda kuwa da ya faru babu shakka zai haifar da wani gagarumin yaƙi a tsakanin ƙuraishawa. Amma sai Allah ya kiyaye, Abubakar ya farfaɗo can a cikin dare. Kalma ta farko kuwa da ta fito bakinsa ita ce, "Ina Manzon Allah?"
Damuna Baki Mugunta
Abubakar ya yi amfani da dukiyarsa wajen sayen bayi, talakawa waɗanda ake azabtar da su a kan Musulunci kamar Amiru ɗan Fuhairata wanda yake ya haɗa uwa da 'yarsa Nana A'ishah. Abubakar ya saye shi daga hannun Ɗufail ɗan Abdullahi ɗan Haris wanda yake azabtar da shi. Sannan Abubakar ya 'yanta shi, ya samu damar yin addininsa har ma ya halarci yaƙe-yaƙen Badar da Uhud, ya kuma samu shahada a yaƙin Mu'unah.
Haka shi ma Bilal Ɗan Abu Rabah (Ladanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama) Abubakar ya same shi ana azabtar da shi sai ya saye shi daga mai gidansa Umayyatu ɗan Khalaf, ya 'yanta shi. Shi ma kuma ya halarci yaƙe-yaƙen Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
Sai Zinnirah, wata baiwar Allah da Umar ɗan Khaɗɗabi ya mallake ta kafin musuluntarsa, ya kuwa rinƙa azabtar da ita har sai da ta rasa idanunta, Sannan sai Mushrikai suka ce, Lata da Uzza sun la'ance ta shi ya sa ta ma kance amma imaninta da Allah ya sa Maɗaukakin Sarki ya mai da mata da ganinta, sai suka ce, wannan yana cikin sihirin Manzon Allah. A kan wannan baiwar Allah da izgilin da mushrikai ke yi wa Musulunci a kanta aya ta sha ɗaya daga suratul Ahƙaf ta sauka. Abubakar ya fitar da ita daga ƙangin bauta don ta samu 'yancin ba da tata gudummawa ga addinin Allah.
Ba waɗannan kaɗai Abubakar ya saya ya 'yanta su saboda Allah ba, akwai wasu bayi daga ƙabilun Banu Adiyyin da Banu Abdi Shamsin su ma sun more ma karamcin Abubakar da kishinsa ga addini wajen samun wannan babbar garaɓasar da yake neman yardar Allah da Manzonsa a kanta.
Wasu daga cikin darajojinsa
Babu wani daga cikin Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wanda ya tara darajoji, musamman waɗanda ya keɓanta da su kamar Sayyadina Abubakar (R.A) Daga cikin darajojinsa akwai tsananin kusancinsa ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da kasancewarsa abokin sirrinsa. Misali shi kaɗai ne wanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sanar da shi yana son Hafsah kafin ya yi maganar aurenta. Ga kuma ayoyin Alƙur'ani da suka sauka suna yaba ma halayensa na jarunta da karimci da tsoron Allah.
Ga shi kuma ya tara dukkan ayyukan alheri da suka sa za a kira shi ta dukkan ƙofofin aljanna, ga kuma fifikonsa na ilimi a kan sauran Sahabbai, domin dukkansu sun aminta cewa, bayan dai ya keɓanta da sanin ilmin nasaba (Dangatakar mutane da sanin tarihin kakanninsu) kuma shi ne ya fi su ilimi daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi mafarkin an kawo masa madara a cikin wata ƙwarya sai ya sha har ta gudana a tsakanin fatarsa da tsokarsa, sannan sai ya bai wa Abubakar. Sahabbai suka fassara wannan da cewa, ilmin da Allah ya ba shi ne ya rage wa Abubakar. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, kun yi daidai! Kun yi daidai!!.
Abubakar kuma shi ne mafi tsentseni da tsoron Allah a cikinsu. Saboda tsentseninsa ne ya taɓa amaye madarar da ya sha domin ya yi shakkar halalcinta. Haka kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba shi shedar tawali'u da rashin girman kai a lokacin da ya ce masa, kai ba ka jan wandonka saboda girman kai. Imaninsa kuwa ya rinjayi na sauran jama'a kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayyana a wurare da dama.
Shi kaɗai ne yake fatawa a gaban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, shi kuma kaɗai ne yake wakiltarsa a abinda ya keɓance shi kamar limancin Sallah da jagorancin Hajji da makamantansu.
Jarumtakarsa da tsayuwar ra'ayinsa
Da yawa daga marubuta tarihi suna kallon Abubakar a matsayin mutum mai rauni, maras kuzari, wanda sanyin halinsa ya rinjayi ƙarfin jikinsa. Sukan ɗauki Umar a matsayin ƙaƙƙarfa, matsananci, mai kazar kazar. Wannan sai ya sa mafi yawan makaranta suka kuskuri fahimtar wane irin mutum ne shi Abubakar.
Ga wasu 'yan misalai a gurguje da za su wargaza wannan gurguwar fahimta nan take:
An tambayi sayyiduna Ali Raliyallahu Anhu wane ne duk ya fi ku jarunta? Sai ya ce, ba shakka ni ban taɓa fito na fito da namiji ba sai na kada shi amma a cikinmu babban jarumi shi ne Abubakar. Sai Ali ya ba da labarin irin bajintar Abubakar a ranar da aka yi yaƙin Badar wanda shi ne karo na farko da Musulmi suka fara sanin yaƙi.
Ba dai wani yaƙin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fita ba tare da Abubakar yana tare da shi ba. Ya kuma shugabantar da shi a kan rundunar yaƙi ba sau ɗaya ba, kuma ba inda ya je ba tare da Allah ya ba shi nasara ba. Misali a shekara ta bakwai bayan hijira shi ya jagoranci rundunar da ta yaƙi Banu Fizarah ya ganimanto dukiyarsu. Sannan shi yake riƙe da tuta a yaƙin da ya fi kowane tsananta a kan Musulmi, shi ne yaƙin Tabuka. A ranar yaƙin Hunaini kuwa Musulmi sun sha wahalar da ta sa akasarinsu suka ja da baya kamar yadda Allah ya faɗa a aya ta 25 a Suratu Ali Imran. Amma duk da haka Abubakar ya tsaya wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana ba shi kariya tare da 'yan kaɗan daga cikin Sahabbai waɗanda suka haɗa da Umar da Ali da Fadlu ɗan Abbas da babansa Abbas da Usamatu da Abu Sufyan ɗan Harisu. To, wane irin kuzari mu ke nema ga wanda yake a duk yaƙe-yaƙe shi ne yake tare da jagoran tafiya Sallallahu Alaihi Wasallama? Wannan shi ne raggo? A dai sake nazari!
Wani muhimmin abu game da Abubakar shi ne kasancewarsa mai tsayayyen ra'ayi wanda ba a saurin girgiza shi. Wannan ɗabi'a ce da ta ke taimakon shugaba ainun. Mu tuna yadda Umar ya rinƙa jayayya da shi a kan yaƙar waɗanda suka soke rukunin Zakka wai da hujjar cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne kawai Allah ya ce ya karɓe ta, tun da kuwa ya cika babu sauran ba da Zakka. A daidai lokacin da Umar ke ganin a dakatar da yaƙarsu har komai ya koma daidai, Abubakar ya nace a kan wajabcin yaƙarsu kuma daga ƙarshe Umar ya gamsu, sannan Allah ya ba su nasara. Abubakar ya kuma yi jayayya da Usamatu ɗan Zaidu da mafi yawancin Sahabbai a kan tafiyar rundunar Usamatu ɗin bayan cikawar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Duk a waɗannan wurare Abubakar shi kaɗai yake a ra'ayinsa, kuma bai ja da baya ba har sai da Allah ya nuna wa mutane cewa ra'ayin nasa shi ne daidai.
Wane irin kuzari muke nema ga Abubakar, mutumin da kowa ya ruɗe a lokacin wafatin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama har ba mai iya ba da sanarwar haka sai shi? wanda ya yanke hanzarin duk mai wata shakka ko mai nufin ya sauya tafiya bayan cikawar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin wannan haɗaɗɗiyar huɗubar tasa? Irin wannan huɗubar ce kuma ya yi wadda ta raba gardama a Saƙifa lokacin zaɓen khalifa na farko.
Daga cikin siffofin jagoranci da Abubakar yake da su akwai zurfin nazari da hangen nesa waɗanda ya same su saboda tsawon daɗewa tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Duba yadda su ka yi da Umar ranar Hudaibiyah, ranar da mushrikai suka hana su shiga garinsu na asali, Makka, wanda suka nufa don su girmama ɗakin Allah, su yi Umrah sannan su koma wurin hijirarsu. A wannan ranar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya hangi wani abin da sauran Musulmi ba su hanga ba wanda ya sa ya ce, a yau duk sharaɗin da suka ba ni zan karɓa. Daga ƙarshe mushrikai suka nemi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kwance haramarsa, ga shi kuwa yana dab da shiga garin Makka. Suka ce, sai ya koma har bayan shekara ɗaya za su yi masa iznin sake dawowa. Suka kuma ɗora masa alhakin mayar da duk wanda ya musulunta daga ranar nan idan ya yi hijira, a yayin da suka sharɗanta ma kansu in wani ya yi ridda ya baro Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba za su mayar da shi ba. Duk dai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce ya yarda. A nan ne Musulmi suka ɗaure fuska, Umar kuwa yazo wajen Abubakar yana so ya yi masa tambaya. Abubakar ya ce, bismillah! Umar ya ce, ashe ba mu muke a kan gaskiya, su suke a kan ƙarya ba? Abubakar ya ce, haka ne. Ashe Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai gaya mana Allah ya yi alƙawarin za mu shiga Masallaci mai alfarma ba? Ya ce, haka ne. To, don me za mu ɗauki wulaƙanci a addininmu?
A nan ne Abubakar ya ce masa, shin ka san cewa shi Manzon Allah ne? Umar ya ce, eh. Ya ce, to, zai saɓa masa ne? Ya ce, a’a. Ya ce, to, da ya ce Allah ya yi mana alƙawarin shiga Makka ya gaya maka cewa a wannan shekarar ne? ya ce, a'a. Ya ce, to, ka jira Allah zai cika ma Manzonsa alƙawarin da ya yi masa, kuma ba zai taɓa tozarta shi ba. Mu lura da irin nazarinsa da hangen nesa da ƙarfin imaninsa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Wannan shi ya sa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fi karkata ga ra'ayinsa idan aka zo wajen shawara kamar yadda ya faru bayan yaƙin Badar game da fursunonin da aka kama, Umar yana ganin a kashe su a huta, a yayin da shi kuma Abubakar yake ganin a fanshe su don a kyautata ma zumunta, a nemi ƙarin ƙarfi da kuɗin fansar, a kuma yi fatar su shiriya a dalilin afuwar da aka yi mu su. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bi shawarar Abubakar.
Tarihin Sayyadina Abubakar Dan Abu Kuhafa Kashi Na Biyar (5)
Abubakar Na Manzon Allah
Nuni ya ishi mai hankali
Tun kafin cikawarsa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayyana ma Musulmi sha'awarsa ga khalifantar da Abubakar a madadinsa. Ga shi dai shi ne Amirul Hajji guda ɗaya da aka taɓa yi a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ga kuma shi an umurce shi da ba da Sallah.
Wasu mutane kuma sun nemi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya faɗa musu inda zas u kai zakkarsu a bayan rayuwarsa sai ya ce, su kai ma Abubakar. A yayin da ya yi ma wata mace hukunci kuwa ya ce mata, ki dawo lokaci kaza, sai ta ce, to in ban tarar da kai ba fa? Tana nufin in rai ya yi halinsa. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce ma ta, sai ki je ki samu Abubakar.
To, in ko har ya kasance Abubakar shi zai jagoranci sallah da hajji da sha'anin zakkah, kuma ya yanke hukunci a tsakanin mutane to, ina wani shugaba ba shi ba?
Wani lokacin ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kan yi umurni da a kira masa Abubakar da iyalansa don ya ba da wasicin gare su amma kuma sai ya fasa yana mai ƙarawa da cewa, Allah ba zai bari a kauce ma Abubakar ba, Musulmi ma kuma ba za su yi hakan ba. Lokaci na ƙarshe da haka ta faru shi ne a daren juma'arsa ta ƙarshe a duniya in da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, a kawo masa takarda zai sa a rubuta alƙawari wanda zai hana saɓani, amma sai sayyiduna Umar ya ce, kar ku matsa ma Manzon Allah, ga littafin Allah a gabanmu, me kuke nema daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama? Ai zafin ciwon da yake fama da shi ya ishe shi. Da aka soma maganganu akai sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, ku tashi ku ba ni wuri! Bai kuma sake wannan maganar ba a sauran wuni huɗu da ya yi bayan haka a duniya.
Abubakar ya zama khalifan farko
Ba zai yiwu ga duk wata al'umma mai cin gashin kanta ba ta wayi gari kuma ta maraita ba wani shugaba a kanta. Wannan shi zai fassara irin hanzarin da aka yi wajen tsayar da wanda zai gaji Manzon Rahmah Sallallahu Alaihi Wasallama.
A yammacin ranar litinin ne wadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya cika a cikinta, Abubakar ya samu labarin cewa, Ansaru, mutanen Madina sun yi gangami a wani waje da ake kira Saƙifa, can arewacin birni, sun fara nazarin sha'anin khalifanci a bayan Manzo Sallallahu Alaihi Wasallama. Kaitsaye Abubakar ya tasar ma wurin wannan taron na Ansar domin ya gane ma idonsa irin wainar da ake toyawa. A tare da shi akwai mutane biyu daga cikin manyan Muhajirai, su ne; Umar ɗan Khaɗɗabi da Amiru (Abu Ubaidata) ɗan Jarrah waɗanda bisa ga sa'a ne ya haɗu da su ba tare da an je nemansu don su halarci taron ba.
Da Abubakar ya iso wurin taron sai ya nemi su gabatar masa da bayanin abin da su ke ciki. Magabata daga cikinsu su ka yi jawabai cike da yabawa ga kawunansu da bayyana irin matsayinsu a Musulunci. Umar ya so a ba shi dama bayan haka ya yi magana, amma Abubakar ya neme shi da ya dakata. Sannan shi Abubakar ɗin ya yi wani gajeren jawabi wanda ya tabbatar ma Ansaru da duk abin da suka faɗi na falala har ma da ƙari a kan hakan. Ya ƙara da cewa, amma kuma kun sani mutane ba za su iya miƙa wuya ga wata ƙabila ba sai ta ƙuraishawa. Wannan shi ya sa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba da umurnin tsayar da khalifanci a cikinsu. Sannan ya tambayi ɗaya daga cikin manyan shugabannin Ansar, Sa'adu ɗan Ubadah (wanda shi ne Ansar su ke son su naɗa a matsayin khalifa) cewa, ko ka ji wannan bayani daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama? Sa'adu ya ce, eh.
Ganin haka ta faru, ga gaskiya ta fito a fili cewa, akwai matsala wani ba Baƙuraishe ba ya jiɓinci wannan lamari, kuma ga umurnin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wanda shugaban nasu ya yi iƙirari a kansa, sai jikinsu ya yi sanyi, ya kasance ba abinda ya rage a kansu sai miƙa wuya ga gaskiya. Don haka nan take Abubakar ya ce ma su, to, in haka ne, ni na aminta ku naɗa ɗayan waɗannan biyu da ke tare da ni Umar ko Abu Ubaidah domin kowannensu ya cancanta.
Faɗin haka da Abubakar ya yi sai wani daga cikin Ansaru ya ce, ni na samar muku da wata mafita mai sauƙi ita ce, a naɗa shugabanni biyu, ɗaya daga cikinku ɗaya daga cikinmu. Sai Zaidu ɗan Sabitu (ɗaya daga cikin Ansar ɗin har wayau) ya ce, a'a, gaskiya dai ita ce, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne ya kasance shugaba, mu kuma mu ne mataimakansa. Don haka, su naɗa khalifa mu kuma mu taimaka masa. A nan ne Umar ya yi wata magana wadda ta daɗa kashe musu jiki baki ɗaya. Ya ce, ya ku jama'a! Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama fa shi ne ya naɗa Abubakar don ya ba mu Sallah. A cikinmu wane ne yake iya mayar da shi baya shi ya shiga gaba?
Da haka dai Umar ya nemi amincewar Abubakar don ya yi masa mubaya'a. Nan take kuma sauran jama'a gaba ɗaya suka mara masa baya ba tare da wata jayayya da ta biyo bayan hakan ba. Washegari ranar talata Abubakar ya zauna a kan mimbari sauran al'umma su ka yi tasu mubaya'a musamman Muhajirai da aka yi wancan taron ba da su ba.
Ko Ali ya yi mubaya'a ga Abubakar?
Manazarta sun ƙari junansu sani a kan wannan magana. Abinda yake tabbatacce dai shi ne, Ali ya yi mubaya'a ga Abubakar amma ba a cikin gangamin farko da aka yi ranar talata ba. To, ko akwai wani jinkiri mai yawa a tsakanin mubaya'arsa da ta sauran Sahabbai? Kuma mene ne dalilin haka? Wannan shi ne muhallin da masana su ke saɓani a kansa.
Akwai dai wata muhimmiyar rana da Abubakar ya yi huɗuba wadda a cikinta yake cewa, Wallahi ban taɓa kwaɗayin sarauta ba a dare ko a safiya, ban kuma taɓa roƙon Allah a kanta ba a sarari ko a ɓoye. Bayan haka ne sai Ali da Zubairu suka tashi suka ba da hanzarinsu ga Abubakar, suna cewa, mu daman mun yarda da cancantarka ga wannan al'amari, domin mun san matsayinka a wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, kuma mun san ya umurce ka da ka bada Sallah, amma mun ji zafin ba a yi shawara da mu ba.
A ruwayar Abu Sa'id al Khudri cewa ya yi, Abubakar ya duba a cikin mutane yana kan mumbari bai ga fuskar Ali ba, sai ya aika kiransa ya ce masa, ya aka yi ka na ƙanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kuma surukinsa sannan ka ke son ka raba kan Musulmi? Sai Ali ya ce masa, kada ka damu, ya miƙa hannunsa ya yi masa mubaya'a.
Daga cikin ra'ayoyin malamai kan fassara rashin gaggawar mubaya'arsa akwai masu alaƙanta shi da cewa, Fatimah (A.S) matarsa ta nemi a raba gadon mahaifinta Sallallahu Alaihi Wasallama domin a ba ta nata kaso. Abubakar kuwa ya sanar da ita abinda ya ji daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa, su Annabawa ba a gadonsu, abin da duk suka bari ya zama sadaƙa ga Musulmi. Fatimah ta yi fushi a kan wannan magana kuma ba ta sake yi masa maganar ba har Allah ya karɓi ranta.
Duk da kasancewar Abubakar ba ya da laifi a cikin wannan lamari, amma an ruwaito ya je ya roƙi afuwarta a kan fushin da ta yi kuma ta yafe masa.
A ra'ayin wasu marubuta, wannan rashin jituwa a tsakanin khalifa da uwar gidan Ali shi ya janyo jinkirin da Ali ya yi wajen ba da mubaya'arsa. To, amma ruwayar da mu ka ambata a baya tana nuna cewa, damuwarsa a kan rashin shawartarsa ne a lokacin da aka naɗa khalifa shi ya kawo jinkirin mubaya’arsa.
Duk yadda al'amarin ya kasance dai, Ali ya yi mubaya'a ga khalifa Abubakar, ko da farko ko kuma daga baya. Kuma ya shiga a cikin sha'anin gwamnatinsa, ya yi yaƙi a rundunonin da su ka yi faɗa da waɗanda su ka yi ridda da waɗanda suka soke rukunin zakka. Kamar yadda ya bada gudunmawa mai yawa wajen tafiyar da mulkin Abubakar ta hanyar shawarwarinsa masu amfani.
Jinkirin da ya yi kuma ba zai kawo giɓi a sha'anin shugabanci ba, domin kamar yadda za mu gani a nan gaba, ba wani shugaban da bai gamu da irin wannan ba har shi kansa sayyiduna Ali a lokacin da nasa khalifancin ya kama.
Ayyukan Abubakar a lokacin shugabancinsa
Duk da ƙarancin lokacinsa, Abubakar ya yi ayyuka masu muhimmanci kuma masu yawan gaske waɗanda suka yaɗa manufofin Musulunci suka kafa daularsa, kana suka ba shi kariya daga sharrin maƙiya.
Tun da farko da karɓar aikinsa sai da ya shigar da duk sauran dukiyar da ya mallaka a cikin taskar gwamnati a matsayin sadaka zuwa ga Musulmi. Sannan ya ci gaba da sana'arsa kamar yadda ya saba. Daga bisani Umar ya lura da rashin yiwuwar haɗa aikin khalifa da kasuwanci inda ya nemi Abubakar ya dakatar da kasuwancinsa a yanka masa albashi. A lokacin da ya buƙaci ƙarin albashi kuwa sai da Sarkin Musulmi Abubakar ya nemi iznin jama'a a kan mimbari suka aminta sai dai wani mutumin ƙauye guda ɗaya da ya ce su ba su aminta ba. Abubakar ya ce masa, ai ku mutanen karkara 'yan amshi ne ga mutanen birni, in sun yarda ku sai dai ku ce Amin.
Abubakar ya kasance mai darajanta Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ƙwarai da gaske. Shi ya sa a lokacin da ya karɓi dukiyar farko a halifancinsa wadda ta zo masa daga Bahrain sai ya shelanta cewa, duk wanda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi masa wani alƙawari to, ya zo mu cika masa. Haka kuwa ya biya duk bashin alƙawurran da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi.
Daga cikin ayyukan khalifa Abubakar akwai tattara Alƙur'ani da ya yi. Wannan kuwa ya faru ne a lokacin da aka ƙarasa yaƙin Yamamah, aka fatattaki sojojin Musailamah, sai Abubakar ya lura da cewa, mahardatan Alƙur'ani da yawa sun kwanta dama. A nan ne ya yanke shawarar a tattara Alƙur'ani wuri ɗaya a matsayin littafi a maimakon a dogara ga mahaddata waɗanda yaƙe-yaƙe na iya kawowa baya gare su.
Kasancewar sahabbai sun tarbiyyantu a kan bin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sau da ƙafa, Umar ya yi jayayya da Abubakar a kan wannan ra'ayi nasa yana mai cewa, ya za ka aikata abin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai aikata ba? Abubakar ya nace a kan ra'ayinsa yana lurar da shi cewa, wannan aikin alheri ne da Annabi zai yi farin ciki da al'ummarsa idan ta yi shi. Kuma ma dole ne a ɗauki wannan mataki don kare shi Alƙur'anin daga ɓacewa.
Wannan hangen nesan na Abubakar ya taimaka ainun wajen sadar da littafin Allah zuwa ga jama'a a wurare daban-daban na duniya ba tare da wani sauyi a cikinsa ba sai fa irin bambancin da ke akwai na karatun wasu kalmomi (ƙira'oi) wanda tun a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ya ba da izninsa don yalwantawa.
Yaƙe-yaƙen da a ka yi a lokacinsa
Abubakar ya karɓi ragamar khalifanci a lokacin da Larabawa su ka yi ridda suka fice daga addinin Musulunci in ban da mazaunan waɗannan birane, su ne; Makka da Madinah da Ɗa'ifa da Bahrain.
Kwarjinin daular Musulunci ya kusa ya tafi ga baki ɗaya daga idon mutane ganin cewa jagoran tafiya ya kau daga duniya. A wannan lokacin ne wasu maƙaryata suka bayyana kamar Al Aswad Al Anasi a ƙasar yaman, da Musailamah Al Thaƙafi a Yamamah, da Ɗulaihah Al Asadi a ƙasar Najdu, dukkansu suna da'awar annabta. Ita ma Sajahi wata mata ce da ta yi irin wannan da’awa ta ƙarya.
Siddiƙu ya fuskanci wannan ƙabubale da zuciya mai ƙarfin imani da nasarar Allah, babu ja da baya.
Tun da farko sai ya zartas da ci gaban tafiyar rundunar Usamatu wadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya aike ta zuwa ƙasashen Balƙa'u a kudancin Jordan da Darum ta kudancin Falasɗinu kusa da yankin Gaza domin su yaƙe su, su yi kira zuwa ga Musulunci. Wannan shawara da Abubakar ya yanke ta gamu da ja in ja sosai daga ɓangaren Sahabbai har ma da shi Usamatu ɗin kansa, ganin cewa yanayi ya canza, ya kamata Musulmi su damu da gyara cikin gida maimakon neman fita waje, kuma musamman ƙasashen da suke cikin riƙon Rumawa ƙasa ta biyu a wajen ƙarfin yaƙi da makamai a duniya.
Abubakar dai bai sauya ra'ayinsa ba yana mai kafa hujja da cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da kansa ne ya nanata batun tafiyar wannan runduna don haka ba abin da zai hana tafiyarsu.
A cikin hikimar Gwanin Sarki wannan shawara sai ta zama alheri ga Musulmi domin kuwa duk in da wannan runduna ta shuɗa sai labarinta ake yi, ana mamakin irin ƙarfin da Musulmi su ke da shi a wannan lokaci wanda ya sa wafatin jagoransu ba ta karya su ba har ma suna nufin shelanta yaƙi a ƙasashen waje. Wannan sai ya maido da kwarjinin Musulmi a idon sauran mutane. Waɗanda kuwa suka yanke shawarar ficewa daga Musulunci sai cikinsu ya ɗuri ruwa suka haƙiƙance ba su iya ja da wannan sabuwar gwamnati, abinda ya sauƙaƙe ma Abubakar samun cikakkiyar nasara a kansu. Bayan kimanin kwanaki saba'in daga fitar rundunar Usamatu sai ga su sun dawo da cikakkiyar nasara da ganimomi masu tarin yawa.
Bayan haka ne Abubakar ya ɗaga tutoci guda goma waɗanda ya zaɓi mayaƙansu da kansa don yaƙi da masu ridda, ya kuma fita da kansa don ganin nasarar waɗannan rundunoni duk da yake Ali Raliyallahu Anhu ya yi ƙoƙarin nuna masa haɗarin fitar da kansa in da ya ce masa, kar ka yi mana hasarar kanka. Irin maganar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gaya ma Abubakar ɗin a yayin da ya ga kuzarinsa da ƙuzaminsa a yaƙin Badar.
Jagororin yaƙin ridda
Fitattun jagororin jihadi a wannan lokaci sun haɗa da Khalid ɗan Walid wanda ya yaƙi ƙabilun Asad da Gaɗfan mabiyan Ɗulaihah Al Asadi, ɗaya daga cikin annabawan ƙarya. A ƙarƙashin tutar Khalid kuwa akwai manyan baraden musulunci cikinsu har da Ali ɗan Abu Ɗalib (R.A).
Daga cikin jagororin har wayau akwai Ikrimah ɗan Abu Jahli da Shurahbilu ɗan Hassanah waɗanda suka yaƙi ƙabilar Banu Hanifah mabiyan Musailimah. Daga bisani Khalid ya karɓi ragamar wannan yaƙin bayan ya gama da mutanen Ɗulaihah da magoya bayan Sajahi ba'annabiyar ƙarya.
Akwai kuma Khalid ɗan Sa'id ɗan Ass wanda ya je iyakokin Sham, da Amru ɗan Ass da ya yaƙi ƙabilar Ƙudha'ah da Ala'u ɗan Hadhrami da ya nufaci ƙasar Bahrain. Wasu tutocin kuwa sun nufaci ƙabilun Hawazin da Banu Sulaim da Kindah da Banu Tamim da ƙabilun Tihama ta ƙasar Yaman da sauransu.
Sahabbai sun gamu da taimakon Allah mai yawa, domin kusan a duk yaƙe-yaƙen da suka je abokan gaba sun fi su yawa, amma ƙarfin imaninsu da Allah da kyakkyawar manufarsu ta kare addininsa ta sanya taimakon Allah ya zamo a gefensu.
Misali a yaƙin da aka fi sani da suna Harbul Yamamah yawan mayaƙan Banu Hanifah ya kai mutum dubu arba'in amma sojojin Khalid ɗan Walid sun daure a kan haɗuwa da su har sai da suka kashe sama da sojoji dubu goma daga cikinsu, sannan suka kai ga Musailimah inda Wahshi ya ɗara masa kibiya wadda ta halaka shi.
Duka duka Musulmin da su ka yi shahada a wannan yaƙi ba su zarce ɗari shida ba. Daga baya ƙabilar Banu Hanifa sun nemi sulhu bisa ga tilas, Khalid ya rattaɓa hannunsa a kan wata yarjejeniya da su wadda a bayanta ne suka musulunta baki ɗayansu. Kafin haka Musulmi sun ganimanci dukiya da bayi masu yawa daga wurinsu.
A cikinsu har da kuyangar Sayyiduna Ali, Khaulatu ɗiyar Ja’afar Al Hanafiyyah wadda ita ce ta haifa masa Muhammad wanda aka fi sani da suna Ibnul Hanafiyyah (Ɗaya daga cikin Imamai ma'asumai a wajen wasu ɓangarori na Shi'a).
Bayan gama yaƙin Ridda
Bayan da Sayyadina Abubakar (R.A) ya haƙiƙance cewa, ya magance matsalar ridda, sai ya mayar da hankalinsa ga faɗaɗa daular Musulunci ta hanyar isar da saƙonsa zuwa sauran ƙasashen ƙetare.
A nan ne fa aka gwabza yaƙe-yaƙe tare da sojojin majusuwa na Farisa da kiristocin Sham. Mafi shahara daga cikin yaƙe-yaƙen da aka yi shi ne yaƙin Yarmuk wanda Musulmi ƙimanin dubu ashirin da bakwai (27,000) suka tunkari rundunar kiristoci mai mayaƙa dubu ɗari da ashirin (120,000).
Musulmi kafin su cimma fagen wannan yaƙi sun gamu da ƙishirwa mai tsanani wadda ta tilasta su yanka raƙumansu don su samu ruwan sha. Haka kuma sun samar da sababbin hanyoyi a cikin sunƙurmin daji don taƙaita tafiya.
An ba da labarin cewa, a cikin wannan yaƙin ne Mahan Sarkin Ruma ya nemi ganawa da Khalid, inda ya nemi ya tozarta Musulmi yana mai cewa, mun samu labarin yunwa ta fitar da ku. Don haka, za mu sallame ku da Dinari goma goma kowannenku. Za mu kuma ba ku tufafi da abinci, mu kuma rinƙa aika muku irinsu kowace shekara.
To, da yake an ce karen bana shi ke maganin zomon bana, Khalid (R.A) sai ya ba shi amsa da cewa, mu ba abinda ya kawo mu ke nan ba. Mu dai a rayuwarmu babu abin da mu ke so kamar shan jinin ɗan adam, sai mu ka sami labarin cewa, jinin Rumawa ya fi kowane jinin ɗan adam daɗi, shi ne mu ka zo mu yaƙe ku domin mu sha.
Faɗin haka sai cikin gogan da na jama'arsa suka ɗuri ruwa, ba tare da ɓata lokaci ba bayan fara yaƙin Rumawa suka rinƙa arcewa suna tsoron a shanye jinin su.
Nasarar Allah ta sauka ga Musulmi nan take
Har wayau a wannan yaƙin ne Sahabbai suka bar wani gagarumin abin tarihi wanda ba a taɓa ganin irinsa ba. Domin kuwa an samu ruwa kaɗan a lokacin tsananin ƙishi amma ya kasance kowannensu yana cewa a kai ma wani ɗan uwansa Musulmi har sai da wasu daga cikinsu suka mutu saboda ƙishirwa alhalin suna zaɓin 'yan uwansu da wannan ruwa.
Ajali Ya kusanto, Abubakar Ya Nemi Shawarar Sahabbai
Lokacin da ciwon ajali ya tsananta ga Sarkin Musulmi Abubakar sai ya tara abokan shawararsa daga cikin Sahabbai ya nemi ra'ayinsu dangane da wanda zai gaje shi.
Gaba ɗayansu sai suka ce, mun ba ka gari, ra'ayinka shi ne namu, kowanensu yana ƙoƙarin ya ture ta daga kansa. Ganin haka sai Abubakar ya neme su da su yi masa jinkiri har ya sake yin nazari.
Bayan haka, sai ya aika aka kira masa Abdur Rahman ɗan Auf ya tambaye shi kai tsaye, mene ne ra'ayinka dangane da Umar? Abdur Rahman ya ce, duk inda ka ajiye shi ya wuce nan.
Sannan ya kira Usman ɗan Affan ya tambaye shi, sai ya ce, baɗininsa ya fi zahiri. Abubakar ya ce masa, ka kyauta ma kanka domin idan ta tsallake shi to ba inda za ta faɗa sai a kanka.
Allah Mai zamani! Mu duba yadda mulki yake abin gudu a wancan lokaci, amma ba da daɗewa ba sai duniya ta canza.
A lokacin rasuwarsa, 'yar' sa A'ishah Uwar Muminai tana zaune a gabansa tana koyi da wani mawaƙi da yake faɗin albarkacin bakinsa game da mutuwa don ta rage wa kanta damuwa. A nan ne Siddiƙu ya ɗaga kansa ya ce da ita, me ya sa ba za ki karanta in da Allah yake cewa
) وَجَاءَتْ سَكْرَةُ الْمَوْتِ بِالْحَقِّ ذَلِكَ مَا كُنْتَ مِنْهُ تَحِيدُ (19)( سورة
Ma'ana
Kuma mayen mutuwa ya je da gaskiya. (Sai a ce masa) Wannan shi ne abin da ka kasance kana bijirewa daga gare shi. Suratu Ƙaf, aya ta 19.
Da ciwonsa ya daɗa tsananta an nemi izninsa don a kawo masa likita, sai ya ce, "Ai likita ya duba ni".
Aka ce, me ya faɗa? Ya ce, "Ya ce: "Ni mai aikata abin da naga dama ne". Yana nufin cewa, Allah ya san halin da yake ciki kuma ba zai fasa abinda ya hukunta ba.
Abubakar ya yi wafati a cikin watan Jimadha Akhir a shekara ta goma sha uku bayan hijira bayan ya yi shekaru biyu da watanni uku a kan wannan muƙami.