Thursday, 7 November 2024

Karanta Tarihin Addinin Sikhism A Takaice Tare Da Hotuna

Tura Wannan Zuwa Ga

Addinin Sikhism ya samo asali ne a yankin Punjab na arewacin yankin Indiya, da Pakistan ta yau, a ƙarni na goma sha shida.


Mabiya addinin Sikhism
Hoto: We Sikhs

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Sikh a harshen Punjabi yana nufin "Mai koyo," kuma waɗanda suka shiga al'ummar Sikh, ko Panth ("Hanyar"), mutane ne da suka nemi jagoranci na ruhaniya.


Sikhs sun yi iƙirarin cewa addininsu ya kasance daban da na addinin Hinduism, duk da haka, yawancin malaman Yammacin Turai suna jayayyar cewar a farkon matakin Sikhism wani ɓangare na cikin addinin Hindu; kwaskwarima ce kawai, sun kafa hujja da cewa wanda ya fara kafa addinin Sikh wato Guru Nanak ya kasance ɗan addinin Hindu sai daga baya ya ware addinin nasa arewacin Indiya.


Guru Nanak ne ya kafa Sikhism kusan shekaru 500 da suka gabata a wani wuri da ake kira da Punjab. Wannan yanki ne wanda ya mamaye wani yanki na Indiya da Pakistan a Kudancin Asiya a yau.


Mene ne Sikhs suka yi imani da shi?


Sikhs sun yi imani da Allah ɗaya ne wanda yake shiryar da su kuma yake kiyaye su.


Sun gasgata kowa daidai yake a gaban Allah.


Iyalai mabiya addinin Sikhism kenan
Hoto: Sikh net

Sikhs sun yi imanin cewa ayyukanku suna da muhimmanci kuma ya kamata kowa ya yi rayuwa mai kyau.


Sun yi imani hanyar yin haka ita ce:


1. Ka kiyaye Allah a cikin zuciyarka da tunaninka a kowane lokaci.


2. Zauna gaskiya da aiki tukuru.


3. Ku yi wa kowa daidai.


4. Ku kasance masu karamci ga waɗanda ba su da wadata fiye da ku.


5. Ku kyautata zamantakewa 

da kowa.


Wanne ne littafin Sikhism Mai Tsarki?


Ana kiran littafin Sikh mai tsarki Guru Granth Sahib. Guru na goma, Guru Gobind Singh, ya ce bayansa ba za a sami wani Gurus ba, maimakon haka, Sikhs na iya duba littafinsu mai tsarki don jagorancin rayuwarsu kamar sauran addinai da ke amfani da Bible ko Kur'ani.


Mata mabiya addinin Sikhism
Hoto: Fun learning workshops

Guru Granth Sahib tarin darussa ne daga Gurus guda goma wato manyan waliyyan addinin inda ake tunanin cewa manyan malaman addinin Hindu da waliyyai musulmai ne suka laɓe suka rubuta shi.


An rubuta shi cikin Punjabi kuma duk Sikhs suna girmama shi a matsayin kalmar Allah.


Ana ajiye shi a kan wani dandali mai ɗagawa a ƙarƙashin wani alfarma a wurin ibadar Sikh.


Duk Sikhs suna cire takalmansu lokacin da suke kusa da shi.


A ina Sikhs suke bauta?


Ana kiran wurin bautar Sikh Gurdwara wanda ke nufin 'Ƙofar Guru'. Gurdwara shi ne kowane gini inda aka ajiye littafi mai tsarki na Guru Granth Sahib.


Suna kuma rera waƙoƙi da addu'o'i daga Gurus. Ana kiran da hakan Keertan.


Yara mabiya addinin Sikhism
Hoto: Khalsa vox


Suna gama bautar za a gabato da abinci kala-kala cikin kowa ya ɗiba da kansa ya ci ya ƙoshi.


Hakan suke kira da suna (LANKAR).


Sikhism shi ne addini na biyar mafi girma a duniya tare da Sikhs sama da miliyan 25 a duk duniya. 


Manazarta


LIttafin SIKHSIMS Na Jagdeep.


Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kullum domin ci-gaba da samun tarihin addinai daban-daban, da waɗanda ku sani har ma da waɗanda ba ku taɓa jin koda labarin su ba.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user