Friday, 1 November 2024

Komai Da Lokacin Shi

Tura Wannan Zuwa Ga

Ba kowa ke son lokacin zafi ba, amma ba ruwan shi yanayin da wannan, da zarar lokacin sa ya yi zai zo kuma ba zai tafi ba har sai lokacin nasa ya ƙare, hakazalika lokacin sanyi, damina da hunturu. 


Komai da lokacin shi
Hoto: Live science

Marubuci:- Buzu Danfillo


Ba sa hana kowa faɗin ra'ayinsa dangane da so ko ƙin su, kamar yadda ba sa bari ra'ayin kowan ya hana su wanzuwa a lokacin wanzuwarsu tare da gusawa a lokacin gushewar su.


Ni kaina da wannan tsari nake aiki, bakinka naka, gaɓoɓina nawa.


Kowa ya sarrafa abun da yake da iko da shi.


Kai ma idan har kana son zama lafiya da lamirinka da nutsuwar ranka, ka koyi rayuwa bisa tsare-tsare da ma'aunanka ba na 'yan zauna-gefe ba.


Idan abu ya kulle maka kai ka nemi shawara. Wannan bisa buƙatarka ne, amma kada ka tanka wa masu cushen shawarar da ba ka nema ba, hasali irin waɗannan sun fi kowa buƙatar shawara a rayuwa.


Ka yi komai a lokacin ka ba a lokacinsu ba, ba tare da neman fahimtar da kowa dalili ko uzurinka ba.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user