Babu amfanin saka damuwa, idan abu ya faru, face fuskantar gaba. Babu amfanin haɗa kanka da wasu, saboda kowanne da irin ƙaddarar sa.
Marubuci:- Muhammad Yahaya Bamalli
Shawarwari na musamman ga duk matashin da ya tunkari shekaru 30 zuwa sama.
Ga su kamar haka:
1. Ka yi iya yinka wajen gujewa bashi, sai idan ya zama dole, kuma da zarar ka samu sukunin biya to ka yi hakan da wurwuri. "Bashi ba ƙaramar barazana ba ce ga ci-gaba".
2. Shin ka san wane ne fallasasshe wanda za a yi ma wasoso ranar ƙiyama? Shi ne mutumin da ya je lahira da Sallah, Azumi, Zakka, Sadaƙa masu kyau amma ya zagi wancan, ya cuci wancan, ya ci kuɗin wancan, sai a kwashe ladarsa a biya su shi kuma a turashi wuta. Allah ya kiyaye mu.
3. Idan Allah ya hore maka aiki ko sana'a, ka dinga aje wani kaso komai ƙarancinsa, a asusun ajiyarka. "Ajiya maganin wata rana".
4. Bala'o'i 7 ne a gaban mu, kuma kowane 1 bai kai na gabansa masifa ba: (1). Mutuwa. (2). Kwanciyar kabari. (3). Tashin ƙiyama. (4). Tsayuwar ƙiyama. (5). Auna aiki. (6). Bada sakamako. (7). Hawa siraɗi. 'Yan uwa mu yi tanadi, mu yi shiri kafin lokaci ya riske mu. Allah sa mu cika da Imani.
5. Kada ka cutar da kowa, ka nufi kowa da alkhairi, domin rayuwar wani ba ta hana taka, samun wani ba ya hana naka, lafiyar wani ba ta cutar da taka lafiyar, abin da Allah ya rubuta kuma ya ƙaddara baya canjawa. To mene ne na hassada da ƙyashi?
6. Aƙalla ka samu abin yi fiye da ɗaya, "Gida biyu maganin gobara.".
7. Ka guji yi wa Allah shisshigi a kan makomar bayinSa, sai Ya yafe masu abin da kake zarginsu da shi, kai kuma Ya ɓata ayyukanka. Ka guji hukunci akan niyyoyin mutane, domin ba ka kutsa zuciyarsu ka ga abinda suka nufa ba.
8. A kowace safiya kafin rana ta faɗi, yi ƙoƙari ka iya wani sabon abu. Wayar da kake riƙewa makaranta ce babba "Ilimi kogi ne".
9. Idan har abinda mutane za su faɗa a kanka shi ne damuwarka, to haƙiƙa ba ka shiryawa rayuwa a duniya ba, domin wanda ya mutu ma bai huta ba a bakunan mutane. Ya Allah ka tsarkake mana zukatan mu, ka sa mu kasance masu faɗar alkhairi akan kowa Amin ya Allah.
10. Aƙalla kowanne mako ɗaya, ka yi ƙoƙarin karanta wani littafi. Akwai darussa da dama ƙunshe a cikin littattafai. "Ilmi haske ne".
11. Waɗanda suka rasu ba su yi gaggawa ba, mu da muke raye ba mu yi jinkiri ba, kowa lokacinsa yake jira. Kuma idan lokacin ya yi ba makawa sai an tafi. Allah ka ɗauki ranmu a lokacin da ka yarda da mu muna masu Imani.
12. Ka dinga motsa jiki aƙalla sa'a (awa) ɗaya a rana. "Mafi yawan cututtuka nada alaƙa da rashin motsa jiki.".
13. Ya kamata jiya ta ba ka darasi ka shiryawa yau, domin dacewa a gobe.
14. Ahir, kashedinka da zaman majalisa, a madadin haka yi wani abin da zai amfaneka da wannan lokacin, kodai koyon wani abu ko neman ilimi. "Zaman kashe wando illa ce babba, kuma hurumi ne na wanzuwar giba da annamimanci". Ba za ka gane muhimmancin lokaci ba sai girma ya same ka.
15. Ya kai Dan Uwa! Da kullum kana tuna masifa da bala'in da ke gabanka na mutuwa, kwanciyar kabari da tashin ƙiyama da ba za ka ɓata lokacinka kana bin diddigin laifuffukan wasu ka manta da kanka ba. Babu mai tambayarka aikin wani a lahira, aikinka za a tambayeka.
16. Ka yi tunani da kyau, mace idan ba mahaifiyarka ba ce ko matarka, ba abin da take ƙara wa rayuwarka sai ɗawainiya da wahala. Don haka ahir ɗinka da neman mata, kodai aure ko kuma sai dai gaisuwa, ko kuma kowa ya yi harkarsa. Ka ji ni ko?
17. Ka dinga tashi tunda safe domin tunkarar ayyukan ka na wannan rana. "Da sassafe ake kama fara".
18. Arziki da ɗaukaka a hannun Allah suke, wanda kake ganin ba kowa ba ne gobe sai ka ga Allah Ya maida shi wani, wanda kake ganin wani ne gobe kuma sai ka ga Allah Ya maida shi ba komai ba.
19. Mace duk nagartarta sai tana ƙaunarka za ka mori zama da ita, don haka ka nemi mai ƙaunarka kuma mai tarbiyya.
20. Ka daina ƙasƙantar da mutane saboda ka fi su matsayi. Idan Allah Ya ga dama gobe sai ka gan ka a ƙasansu.
21. Duk inda ni'ima take dole a tarar da
mahassada.
22. Ba abinda ke da rashin tabbas kamar wannan rayuwar. Komai mai iya canzawa ne a kowanne lokaci.
23. Kowane yini/wuni kafin rana ta faɗi, yi ƙoƙari ka taimaki wani, koda sadaka koda shawara kai koda da bai wa ƙadangaru ruwan sha ne. Kar ka manta, wata karuwa ta samu gafarar Allah sakamakon yin taimako irin wannan.
24. Idan ba za ka iya yaɗa alheri ba kar ka taimaka wurin yaɗa sabon Allah a doran ƙasa.
25. Tallafawa iyayenka da komai ƙanƙantar abin da Allah ya hore maka, koda kuwa suna da sukuni. Akwai albarka sosai a taimakawa iyaye da yi musu biyayya.
26. Duk inda ɗaukaka take dole a tarar da maƙiya, kai dai ka riƙe addu'a.
27. Kada ka riƙa tallata talaucinka a wurin da babu maganin shi.
Haƙuri wata babbar baiwa ce ba kowa ALLAH yake azurta shi da ita ba, sai ɗaiɗaikun mutane.
Kowane Ɗan-Adam mai kuskure ne, sai da yafiya da haƙuri ake zama lafiya da mutane.
Duka waɗannan shawarwarin matakan nasara ne.