Wednesday, 27 November 2024

Nazarin Gane Kishiyoyi A Kasuwanci Don Samun Nasara

Tura Wannan Zuwa Ga

Assalamu alaikum, idan sana’arka ta daɗe da kafuwa, ko kuwa sabuwa ce, ɗaya daga cikin matakai masu muhimmanci domin yin nasara shi ne abin da ya ba ka tagomashi kuma ya bambanta ka da sauran kishiyoyi.


Nazarin Gane Kishiyoyi A Kasuwanci Don Samun Nasara
Hoto: LinkedIn

MarubuciBello Galadanchi


Hanyar gudanar da haka shi ne nazartar kishiyoyin ka. 


Shin wane ne yake gasa da kai wajen ɗaukar hankulan kwastomomi da karɓar kuɗin su?


Shin sana’ar su irin taka ce sak ko kuwa wata irin sana'a ce ta daban amma yana kama da naka?


Mene ne ƙarfin su da gazawar su?


Yaya sauran jama’a suke kallon su?


Alal misali, ba’amurken da ya jagoranci nasarar gidan abinci na McDonalds Ray Kroc, an samu labaran cewa ɗaya daga cikin hanyoyin samun nasarar sa shi ne ya kan bi sharar sauran gidajen abinci yana bincikawa.


Amma akwai sauran hanyoyi masu sauƙi da masu sana’o’i za su iya bi domin fahimtar sana’ar su, kasuwar su da kishiyoyinsu. 


NAZARIN ƘARFI, GAZAWA, DAMARMAKI DA ƘALUBALE (NAZARIN KGDK)


Hanyar da aka fi sani a duniya da masu sana’a ke amfani da ita ana ce mata Nazarin KGDK (Nazarin ƙarfi, gazawa, damarmaki da ƙalubale). Wani manazarcin bunƙasa sana’a ne daga Amurka mai suna Albert Humphrey ne ya ƙirƙiro wannan dabara a shekara ta 1966, kuma ya yi amfani da ita domin fahimtar ƙarfi ko tagomashin sana’a, da inda ta gaza, da kuma irin damarmakin da za ta iya samu, da kuma ƙalubalen da za ta iya fuskanta.


A cikin batutuwan da yake dubawa shi ne ƙwarewar mai tafiyar da sana’ar, ƙwarewar ma’aikatan wannan sana’a, ingancin hajar sana’ar, kuɗaɗen da sana’ar take da shi, da shaharar wannan sana’a, ragowar batutuwan su ne irin damarmakin da sana’ar take da shi na bunƙasa da ƙara adadin kuɗaɗen shiga, ko kuma ƙalubale da ke danno kai kamar sababbin ƙirkire-ƙirƙire, rashin samun hanyoyin shiga wasu kasuwannin, yin ciniki da kwastoman da ke da nisa, da kuma sauyin ɗanɗano na kwastomomi.


DUBA WANNAN: Kalli Zafafan Hotuna Tare Da Tarihin Bello Galadanchi/Dan Bello


Shugabannin kamfanoni da sana’o’i da yawa na amfani da Nazarin KGDK ne wajen fahimtar halin da sana’ar take ciki. 


Babban abu mafi muhimmanci shi ne tasirin wannan nazari wajen ganin mai sana’a ya yi amfani da shi wajen ɗaukar matakin da zai bunƙasa masa sana’arsa. 


Duk yawa da girman bincike na wannan nazari ba shi da amfani idan mai sana’ar bai iya warware shi ya fahimce shi sosai ba ta yadda zai shirya matakan ɗauka domin bunƙasa sana’ar da ƙara adadin kwastomomi da kuɗaɗen shiga.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user