Thursday, 7 November 2024

Ribar Da Za Ku Samu Idan Ku Bambanta Sana'ar Ku Da Ta Kowa

Tura Wannan Zuwa Ga

Ina so na ba ku labarin wani kamfani mai suna Snapple, kamfanin ya yi fice a ɓangaren shayi da lemon kwalba, kuma ya yi nasarar samun gurbi a kasuwa inda yake tsallake wa wajen adana riba mai tsoka.


Ribar Da Za Ku Samu Idan Ku Bambanta Sana'ar Ku Da Ta Kowa
Hoto: Centsand beyond

MarubuciBello Galadanchi


Idan ka shiga shagunan kayan abinci a Amurka, za ka ga lemo da shayi iri-iri daga kamfanoni masu yawa da ke gasa da juna wajen ciniki. Kamfanoni da yawa sun karye a wannan fanni saboda tsabar gasa. Misali, kamfanin Pepsi duk girman sa da sunan sa ya yi ƙoƙarin samun gurbin kasuwa a wannan fanni inda ya ƙirƙiro wani lemo mai suna AM don a ringa shan sa da sanyin safiya, amma babu kwastomomi a wannan gurbi. 


Nasarar kamfanin Snapple ya zo ne a dalilin daidaita kayan su a kasuwa a matsayin daban da saura, kuma suka tallata shi da ikirarin cewa lemo da shayin su sun yi fice. Snapple yana ɗaya daga cikin kamfanoni na farko da ya sarrafa lemon sa baki ɗaya daga ‘ya’yan itatuwa ba tare da gauraya su da sinadari ba.


A shekarun baya, mutanen da suka samar da shi sun gudanar da sana’ar sayar da magungunan lafiya a birnin New York, inda suka yi amfani da taken “Komai namu 100 bisa 100 daga ‘ya’yan itatuwa ne”. Kuma sun mayar da hankali ne akan ɗalibai da ma’aikata masu kai-kawo kullum tsakanin gidajen su da ma’aikatun aikin su. Saboda haka sai lemukan su suka samu farin jini saboda masu saye sun yi imanin cewa lemon ba shi da illa ga lafiyar su, musamman yadda ya zo a cikin ɗan ƙaramar kwalba yadda za’a iya shanye shi a zama ɗaya.


Kamfanin ya sayar da lemon ne a shaguna da ke cikin birni inda babu wahala kwastoma zai shiga, ya siya, ya fita a ɗan ƙaramin lokaci. Waɗannan dabarun sun sa Snapple yana ta samun ciniki babu kakkautawa, kuma kamfanin yana ta samun riba mai nauyi, ga shi kuma ya bambanta sosai daga abokan gasa a shekarun 1980s da 1990s. A shekara ta 1994 kaɗai, Snapple ya yi cinikin dala miliyan 674. 


Samun gurbi a kasuwa wanda babu wanda yake ciki na kawo damar yin arziki da samun nasara ga kamfanoni, amma babban ƙalubalen shi ne gano ko wani gurbin kasuwa ne za’a iya samun riba a ciki, kuma wanne ne tarko?

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user