Ke ce farin cikina da annashuwata. Ina nan riƙe da amanar son ki har ƙarshen rayuwata, ba zan taɓa bai wa kowa ba sai ke kaɗai.
Saƙon zuciya ga masoyiya
Hoto: Marriage
Marubuci:- Rabs
Masoyiya, son ki a gare ni tamkar wani kyakykyawan fure ne da idanuwana ke fara ƙawatuwa da duban shi, hanci ya ji daddaɗan ƙamshin shi, ruhi ya yaba rai ya aminta.
Aminci ya tabbata a gare ki mai sona, ina son ki kamar yadda kike sona, ina tare da ke a kowanne yanayi domin kina kyautatawa zuciyata, kina ba ta farin ciki, duban ki kan kauda lalaci, sanadin son ki rayuwata ta sauya.