Sunday, 24 November 2024

Salon Fara Magana Da Budurwa A Ganin Farko A Aikace

Tura Wannan Zuwa Ga

Saurayi: Assalamu alaikum.


Za ta kalle ka da gefen ido, sannan ta amsa maka. "Wa alaikassalam."


Saurayi: Don Allah idan ba za ki damu ba ina so ki ɗan ba ni minti biyu daga cikin lokutan ki.


Salon Fara Magana Da Budurwa A Ganin Farko A Aikace
Hoto: Zaufishan

Marubuci:- Ridwan Khan Adam


Za ta yi maka musu ta faɗa maka cewa "Gaskiya sauri nake ba na son ɓata lokaci."


To kada ka damu.


Saurayi: Don Allah ki yi haƙuri wata magana nake son na faɗa miki.


Za ta kalle ka sama da ƙasa ta faɗa ma cewa "Ina sauraron ka". Ta ɗaga kai sama.


Saurayi: Haƙiƙa ɗabi'unki da riƙon addininki sun daɗe suna birgeni, a kullum na gan ki sai na ji son ki yana ƙara mamaye zuciyata, idan ba za ki damu ba ina so ki ba ni sarari a cikin zuciyarki domin na samu na kasa hajata, kuma na tabbata zan ci ribar soyayya da ƙauna a cikin zuciyarki.


Za ta ɗan yi murmushi sannan ta ƙara kallonka sama da ƙasa a daidai wannan lokacin ne wankanka zai ɗan yi tasiri kaɗan.


Bayan ta gama yi maka kallo a tsanake za ta mayar maka da amsa kamar haka "Gaskiya ku samari ba abin yarda ba ne, sai mutum ya ba ku dama sai ku yaudare shi ku bar shi a cikin damuwa." .


Saurayi: Haba ya za a yi na yaudari kyakkyawar budurwa kamarki? Ai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba, wallahi son ki nake yi har zuciyata, a kullum da tunaninki nake kwana nake tashi.


Za ta yi maka ɗan murmushi kaɗan wanda ba zai sa ka rainata ba, sannan ta faɗa maka cewa sai na yi shawara.


Saurayi: Shawara? To shikenan, ina sauraron ki duk lokacin da kika gama shawarar amma ina so ki yi min wata alfarma guda.


Za ta tambaye ka, "Wacce irin alfarma?"


Saurayi: Ina so ki sanar da ni duk hukuncin da zuciyarki ta yanke, ni kuma na yi miki alƙawarin cewa koda bai yi mini daɗi ba, zuciyata da idanuwana ba za su taɓa ganin baƙinki ba.


Za ta yi murmushi, ta ce "Kada ka damu da yardar Allah zan sanar da kai".


Saurayi: Hmmn na gode sosai.


Budurwa: Insha Allah babu abin da za ka ji sai alkhairi.


Insha Allah ka sace zuciyarta kenan.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user