Zaman gida saboda annobar cutar COVID-19 na da matuƙar ƙalubale ga jama’a da ma tattalin arziki, saboda ƙarancin kuɗaɗen shiga musamman ga masu ƙananan sana’o’i da masu ƙananan aiki da neman kuɗi a waje.
Marubuci: Bello Galadanchi
Ga wasu sana’o’i da za’a iya yi a lokacin da ake zaman gida:
1. KOYARWA: Ganin cewa an rufe makarantu, ɗalibai yara masu matuƙar yawa suna gida, kusan kuma za’a iya cewa babu abin da suke yi banda wasa, bacci, cin abinci, wasa da waya, kallo da hira.
Kowa da irin baiwar da Allah Ya ba shi. wata ta iya girki, ko kwalliya, wani ya iya lissafi ko turanci, wata ta iya ɗinki ko ilimin zama da raya iyali, wani shi kuma karatun Al-Qur’ani ya iya. Yi amfani da wannan dama domin taimaka wa iyaye da yawa waɗanda ke fama da ƙalubalen kula da yara da ma sauran jama’a da ke zaman banza, ta hanyar ganin cewa suna ci-gaba da wasa ƙwaƙwalwar su da ƙaro sani.
Za’a iya gabatar da waɗannan darussa ta shafin WhatsApp, kuma duk mai buƙata ya biya kuɗi, a saka shi a ciki.
2. HAƊA BIDIYO KO SAUTI: Duk da cewa jama’a da yawa suna haɗa bidiyo da sauti, akwai dama mai yawa a wannan ɓangare.
A daidai wannan lokaci da jama’a suke rufe a cikin gidajensu, suna buƙatar kallo ko sauraren abubuwa iri-iri domin saka zuciyoyinsu cikin nishaɗi da walwala. Me zai hana ka haɗa bidiyo ko sauti na addu’o’i, ƙarfafa zuciya, ilimantarwa ko ma na ban dariya? Kowa na buƙatar wani ɗan abu da zai ba shi dariya a yau da kullum.
Duk wanda yake son shiga group, sai ya biya wani abu a saka shi.
3. SHAGON GWANJO DA TSOFAFFIN KAYA AKAN YANAR GIZO: A halin yanzu da shaguna, kasuwanni da sana’o’i suke rufe, wannan ya kawo babbar damar na gina shagon yanar gizo na sayar da kayan da aka yi amfani da su. Tunda yanzu akwai lokacin gyaran gida, da goge-goge da wanke-wanke, na tabbata akwai kayan da ba’a amfani da su kuma za’a iya tallata su akan yanar gizo ga wanda yake buƙata komai sauƙin su da tsufan su.
Kuma akwai mutanen da idan ba su kashe kuɗi ba, ba sa jin daɗi.
Wannan babbar dama ce ta fara irin wannan kasuwanci.