Kar ka zurfafa soyayyarka ga abin da ba ka da tabbas a kansa, domin soyayya ta zama tamkar ruwan sama ne a yayin da yake sauka daga sama zuwa ƙasa, wanda babu tabbas akan yanayin shi.
Marubuci: Imran Musa Jahun
Akwai lokutan da yake kasancewa ruwan sama ya zo da ƙarfi, kar ka bayar da amannar cewa da ƙarfin za'a ɗauke shi, akwai lokacin da ruwan sama zai sauka a hankali kar ka bayar da gaskiyar cewa a hankali zai ɗauke.
Ka kwatanta waɗannan misalan a matsayin soyayyarka, babu tabbacin yadda ake son ka da farko haka za'a ci-gaba da sonka har abada. Don haka soyayya ba ta da tabbas.
Idan ka ɗauki soyayya da zafi, tamkar kana matsanancin gudu ne kan titi cikin duhun daren da ba za ka iya koda ganin hannunka ba, kenan a kodayaushe za ka iya faɗawa rami ko ka haɗu da abin da ba ka yi tsammani ba.
Haka soyayya ta ke, sai da lura.