Saturday, 30 November 2024

Soyayya Mai Tashi Lokaci Zuwa Lokaci

Tura Wannan Zuwa Ga

Za ka samu wasu masoyan suna gudanar da soyayyar kamar tashin kumfar omo. Kumfa ba a ganinsa sai an haɗa shi, kuma da zarar an haɗa shi yake tashi ya yi sama yana sheƙi da ƙyalƙyali. Bayan wani ɗan lokaci kuma sai ka ga yana yin ƙasa-ƙasa da kansa ba tare da ana so ba sai dai idan wani lokacin amfanin ya taso sai a kuma haɗa wani.


Soyayya Mai Tashi Lokaci Zuwa Lokaci
Hoto: Vocal

MarubuciNura Nakowa


To haka rayuwar wasu masoyan take, haka za ka ga suna gudanar da soyayyar su lokaci zuwa lokaci. Allurar soyayyar su ba ta tashi sai sun ga juna. Idan kuma suka rabu sai a ɗauki tsawon lokaci ba a haɗu ba, kuma fa kar ka ce suna raya soyayyar ta wata hanyar ta daban ce a'a, kawai dai sun tafi kenan tamkar ɗaukewar wutar NEPA sai wani jiƙon idan an sake haɗuwa.


A duk lokacin da suka haɗu za su yi ta cin soyayyar su kamar babu kamar su a duniyar so.


Irin wannan soyayyar ba wai sai da akwai matsala a tsakanin masoyan ake samun haka ba. Wata ƙila wani dalili ne na ƙashin kai, ko sabgogi ko kuma zarafin rayuwa, su suke sanyawa ake samun hakan. Wani sa'ilin kuma rashin maida hankali ne ga wanda ake soyayyar da shi da kuma rashin shiri, wato an shiga soyayya ba tare da an shirya yin aure ba ko kuma ba a da lokacin da za a tsaya a gina soyayyar yadda ya kamata.


To babban abin da ke janyo irin haka shi ne:-


1. Rashin tsayayyan masoyi ko manemi.


2. Rashin tsayar da maganar aure a tsakanin masoyan.


3. Rashin kulawar iyaye na idan za a yi, a yi. Idan kuma ba za a yi ba a san matsayin da ake kai.


Wasu masoyan irin waɗannan kuma suna matuƙar son junansu kuma ba sa kula wasu amma kuma za ka ga ana samun irin wannan soyayyar ta tashin kumfar omo. 


Abin da ke faruwa shi ne, za ka ga wata ƙila da akwai wasu 'yan rigingimu ko wasu matsaloli na gida waɗanda ya kamata a ce an kawar da su (kamar son a haɗa auren dangi ko auren zumunta ko kwaɗayi ko buri) to amma matsalolin ba su kau ba sai ka ga masoya sun daɗe a cikin irin wannan halin.


Akwai waɗanda na sani shekaru biyar zuwa shida su ka yi a cikin irin wannan yanayin.


To abin da ya fi shi ne, idan an shiga so to a kula da shi domin so ba abin wasa ba ne.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user