Monday, 18 November 2024

Tafiyar Da Rayuwa Cikin Nasara

Tura Wannan Zuwa Ga

Kar ka taɓa jin tsoron rashin nasara ko faɗuwa, faɗuwa da rashin nasara waɗannan duka sunna ce ta rayuwa, saboda su suke taimakonmu wajen girmanmu. Kar ka kuskura ka ji tsoron faɗuwa ko rashin nasara akan wani abu saboda wani lokacin sai ka faɗi kake koyon wani sabon abun, sai ka rasa abu kake sanin muhimmancin shi.


Tafiyar da rayuwa cikin nasara
Hoto: Mohammadimran229182

Marubuci:- Usman Yanmaza


Kar ka rinƙa haɗa kanka da sauran mutane, dole ne wani ya fi ka kuma kai ma ka fi wani, kowa yana da irin nasa abun na musamman da sauran mutane ba su da shi, abu mai muhimmanci shi ne ka maida hankali wajen cimma abubuwan da ka saka a gaba kar ka damu da na wasu.


Ka ringa ɗaukar darasi daga kurakuranka. 


Kowa yana kuskure a rayuwa, abu mai muhimmanci shi ne ka ringa ɗaukar darasi a kurakuranka hakan zai ba ka damar gyara gaba domin kauce ma hakan.


Ka yarda da kanka kawai shi ne babba a rayuwarka. Musamman idan ka saƙa wani burinka, ka yarda cewa watarana za ka cimma burinka akan hakan, sannan ka tabbatar kana aiki tuƙuru wajen cimma hakan. Kar ka zamo mara buri.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user