Thursday, 14 November 2024

Takaitacciyar Wasikar Neman Soyayya Ga Sabuwar Budurwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Wasiƙar soyayya zuwa ga masoyiyata.


Adireshi: Lamba 0201 Ceɗiyar 'yan gurasa, Kano.


Kwanan wata: 12/April/ 1996 wanda ya zo daidai da Jimadalllahir hijira 1416.


Zuwa ga Laure Amadu Makwarari, Kano.


Bayan dubun dubatar gaisuwa tare da fatan alkhairi har zuwa Juma'ar da ba ta da asabar. Da fatan kina lafiya kamar yadda nake lafiya. Allah Ya sa haka amin.


Wasiƙar neman soyayya ga sabuwar budurwa
Hoto: Freepik

Marubuciya:- Rahma Abdulmajid


Bayan haka, na san za ki yi mamakin ganin wannan wasiƙa tawa a yau, sai dai ba abin mamaki ba ne idan na gaya miki cewa a tun ranar da na fara ganin ki a layin 'yan ƙosai, kibiyar son ki da ƙaunarki ta huda zuciyata ta gaba ta fito ta baya, zuwa yanzu babu abin da nake fata kamar ganinki da jin ki da sauraren ki.


Wannan shi ne halin da zuciyata ke ciki, da fatan ba za ki watsa min ƙasa a ido ba. 


Allah Ya kai damo ga harawa, ko bai ci ba ya kwanta.


Na gode.


Naki har abada.


Lawandi Ashiru.


Nake cewa ki huta lafiya ya ƙanƙarar firjin zuciyata.


Yanayin yadda ake rubuta wasiƙar soyayya kenan a 90s.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user