Na kamu da son ki da irin shauƙin da babu waige a cikin sa, babu wata tsoka ko jijiyar da ba ta yi mubaya'a ga soyayyar ki ba matuƙar a jikina take.
Tsantsar kalaman nuna damuwa ga masoyiya
Hoto: Goran13/iStock photo
Marubuci:- Ebra Dandume
Ban taɓa zaton so zai illatani haka ba.
Da a ce ana bada amanar rai da tabbas zuciyata ke ce ta amincewa mallakawa nawa ruhin.
Ba don daga Allah ba ne da sai na dakatar da ziyarar da zuciyata ke yi wa taki.
Ki sani har yanzu ina son ki, amma ki sani kin yi mini illa.
Kamannina sun sauya zuwa siffar damuwa, tun ina iya share hawayena har sun ƙare saboda tsananin illar da son ki ya yi mini.