Wasiƙa zuwa gare ki tsohuwar matata.
Ba wai na ce ki dawo gare ni ba ne tunda na san cewa yanzu kin zama mallakin wani. Ina son na sanar da ke cewa sai bayan babu ke na gane cewa ke ba mata ce kawai a gare ni ba, ke kwafin mahaifiyata ce bisa yadda kika kula da ni kamar yadda kike ƙoƙarin kula da abin da muka haifa tare.
Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint
Wannan Abdallah Aliyu da kika sani a da wanda ake yi wa laƙabi da Audu Ba Ka Ji yanzu tuni na daina rashin ji, kuma yanzu tuni duniya ta gaya min, na ji jikina ya yi sanyi kamar yaron da aka ƙwacewa alawa yana cikin tsotsa.
Na daku kamar baƙin ƙarfe a maƙera, na caku kamar sabon mai shan wiwi, na zama salihi kamar limamin masallacin kandahar na rijiyar lemo.
Na tuba na bi Allah kamar marayan da uwarsa da ubansa suka mutu suka bar shi a tsakiyar Sahara.
Rayuwa ta yi min ɗaurin goro gaba da baya, sai da lokacin da na fi buƙatarki a rayuwa ya yi, sannan na neme ki na rasa kamar ɗaukewar wutar lantarki a arewacin Najeriya.
Yanzu na gano kyawawan halayenki wanda na tabbatar da lokacin Sahabbai kika zo duniya tabbas Allah zai yi kyautarki ne ga mafi kyawun tsarki daga Sahabbai ko tabi'ai , tabbas sai sunanki ya fito a cikin littattafan addini saboda kyawawan ɗabi'unki.
Na bar ki lafiya ki ci gaba da more rayuwar aure mai daɗi cikin gidan sabon mijinki, amma na godewa Allah da ya sa na kasance wanda suka taɓa rayuwa da mace mai tsarki kamar ki.
Daga tsohon mijinki.
Abdallah Aliyu Saint, wanda aka fi sani da Audu Ba Ka Ji a shekarun baya.