Monday, 18 November 2024

Wasikar Soyayya Ta Musamman Daga Ustazi Zuwa Ga Ustaziya

Tura Wannan Zuwa Ga

Buɗaɗɗiyar wasiƙa ce zuwa ga masoyiyata, abar begena.


Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakaatuhu, 


Ina rubuta miki wannan wasiƙa a lokacin da zuciyata take cike da ɗimbin ƙauna da begenki. 


Wasiƙar soyayya ta musamman daga Ustazi zuwa ga Ustaziya 
Hoto: Jet-po/Freepik

Marubuci:- Umar Shehu Zaria


Duk lokacin da na tuna da ke sai na ji babu abin da ke mun daɗi a duniya kaf idan ban ji labarinki ba.


Ya sanyin zuciyata, Wallahi zan shiga halin ni-'yasu idan na rasa ki.


Wato ba ni da wasu kalmomi da zan iya miki bayanin irin ƙaunarki da ta ɗarsasu a birnin zuciyata, sai dai na yi alƙawarin zan dage tuƙuru wajen ganin na tara sadakinki mai matuƙar yawa, ina fatan ke kuma za ki tanadar min masauki a farfajiyar zuciyarki.


A ƙarshe ba ni da wasu kalmomi da za su iya bayyana miki irin ƙaunar da ke tsakanina da ke, sai idan mun haɗu za ki gani in sha Allahu Ta'ala. 


Na gode masoyiyata.


Naki:


Umar Shehu Zaria.


Zuwa:


Jannatul Firdausi.


Sauran bayanin ki bari sai mun haɗu ranar alƙiyama, in sha Allahu ta'ala.


ƘARIN BAYANI


Wannan wasiƙar a zahiri ya rubuta ta ne ba zuwa ga masoyiya (Mutum) ba, ya rubuta ne zuwa ga Aljanna, amma za ku iya juya ta zuwa ga masoyiyar ku (Mutum), idan har ta burge ku.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user