Monday, 11 November 2024

Wasu Lokuta A Rayuwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Wataƙila sadaka ko kyautar ₦10 ba komai ba ce a wajen ka, har ma za ka yi tunanin ko ka bayar babu abin da za ta yi ma wanda ka ba shi, amma ba ka sani ba shi abin da yake nema kenan ya fita daga matsalar da ya samu kansa a ciki. Don haka da zarar ka ji zuciyar ka ta yi tunanin aikata alkhairi to ka zartar a aikace kawai, ba lallai ka sake samun wannan damar ba.


Wasu lokuta a rayuwa
Hoto: Yacobchuk1/Depositphotos 

Marubuci:- Muhammad Yahaya Bamalli


Saboda haka kada ka ƙaskƙantar da duk abinda ka ga wani yana so, kada ka wulaƙanta abin da wani yake buƙata, kuma kada ka raina abin da za ka taimaka wa bayin Allah da shi.


Wani lokaci a cikin rayuwa abinda ba ka buƙata, abinda ba ka ɗauke shi a bakin komai ba, shi ne abinda wani yake buƙata ya rayu cikin kwanciyar hankali, abin da bai da sauran amfani a wajen ka shi ne abin da wani yake nema ya tsira a rayuwa.


Wani idan bai samu wannan abin ba zai iya tagayyara a rayuwa, ko kuma ya faɗa cikin hatsari ko ya mutu, abinda ba ka bukata, abin da ka fi ƙarfin sa a yau, wani kuma idan ya samu, ya samu abin da zai rayu da shi cikin kwanciyar hankali kenan.


Abin da za ka bayar ɗin wataƙil shi ne fata na ƙarshe da wani da ke cikin wata rayuwa me ƙunci yake buƙata ruwa a jallo.


Wani yana ciwon kai, ba don ₦20 da ka taimaka masa da ita ya sayi magani ba da wataƙil ajalin sa kenan.


Rigar da kake ganin ka gama amfani da ita, saura ka jefar a bola, wani kuma da zai same ta zai je Masallacin Idi ko wajen ɗaurin auren sa da ita cikin alfahari da jin daɗi a zuciyarsa.


Kada ka jefar, ka yi kyauta, ka yi sadaka ɗan uwa, wani yana buƙata.


Kada ka raina abin da za ka bayar ma wani, ba ka san tasirin abun a wajen wanda za ka ba shi ba, ba ka san ƙarfin abin da ka bayar a can sama wajen Ubangiji ba.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user