Neman kuɗin su
Masu kuɗi babu wani lokaci da ba sa neman kuɗi, har lokacin da suke bacci, saboda suna amfani da mutane da kuma tsari ta yadda sana'ar su ba ta buƙatar ƙarfin su ko lokacin su kafin ta kawo musu kuɗi.
Marubuci:- Abubakar S. Wali
Kashe kuɗaɗen su
Masu kuɗin gaske suna amfani da kuɗin su ne wajen neman wasu kuɗin, ba sa amfani da kuɗin su wajen burge mutane ko nunawa suna da kuɗin. Ba a ganin kuɗin su sai a cikin buƙatar dole ko buƙatar juya kuɗin ta taso.
Mu'amalar su
Masu kuɗi su kan fi yin mu'amala da mutane irin su, masu tunani da manufa irin su.
Lokacin su
Da yawan mu muna musayar lokaci ne domin mu samu kuɗi, amma masu kuɗin gaske suna musayar kuɗi ne domin su samu lokaci, lokacin da suke canjin kuɗi da shi kodai ya kasance lokacin hutu ko kuma lokacin neman wasu kuɗin.
Misali masu kuɗi sun zaɓi su biya wani ya musu wani aikin da za su iya saboda su amfani lokacin ta wani ɓangare.