Mutane da dama masu fassara soyayya sun yi iya ƙoƙarin su gurin bayyana ma duniya yadda so yake shiga zuciyar Ɗan Adam. Yana da kyau idan saurayi ya ga yarinyar da yake so ko ke budurwa idan kin ga saurayin da kike so to ki yi ƙoƙari ki bayyana masa domin barin abin a zuciya zurfin ciki kenan, kuma zurfin ciki a soyayya babbar illa ce domin ya kan iya haifar da ciwon zuciya, wani lokaci har a rasa rayuwa amma yana da kyau kai nazari akan abin da za ka faɗa wa masoyi kafin ka tunkare shi.
Marubuci: Abu Aishert Mallam Madori
Fa'idar yin tunani a tsakanin masoya
Yin tunani akan masoyi kafin a aminta da soyayyar shi yana da kyau matuƙa domin bai wa zuciya damar gano cewa mutumin nan da yake ƙoƙarin ƙulla soyayya da ni mutum nagari ne, sannan tsakani da Allah yake son ƙulla soyayyar kodan cimma manufarsa.
Idan kin kammala tunani, kin gano hallayarsa daga cikin biyun nan dana lissafo kin gano cewa mutum nagari ne kin ga kenan za ki iya soyayya da mutum nagari ba asara ba ce morewa ce, idan kuma kin gano cewa mutumin banza ne to ƙaurace masa shi ne mafi alkhairi a gare ki, kar ki tsaya kina tunanin wai sai kin tatse shi, kar ya je garin jiran tatsar shi shi ya tatse ki ya wuce.
So mai shiga zuciya a hankali
So mai shiga a hankali, yana ginuwa a zuciya ne yayin da masoyi yake kyautatawa wanda yake so, gurin nuna mata gaskiya da riƙon amana, yaba mata da nuna mata tsantsar soyayya, yaba kwalliyarta, da tsuma ta da kalaman soyayya masu daɗi, kyauta da kuma karɓar uzuri. Waɗannan ababen da na lissafo na ɗaya daga cikin ababen da ke sa soyayya ta kutsa kanta cikin zuciya a hankali ta samu guri ta zama ingarma gagara sara ba tare da zuciya ta ankare ba.
Gaskiyar al'amari so mai shiga a hankali shi ne ya fi ɗorewa ya fi daɗewa domin shi ne ke tafiya da ƙaunar juna. Yadda so mai shiga zuciya a hankali yake shi ne soyayyar da saurayi zai ga yarinyar da ta masa ta kwanta masa a rai ya isar mata da saƙonsa cikin hikima da ba ta uzuri ta yi tunani kafin ta ba shi masauki a zuciyarta.