Tuesday, 5 November 2024

Yadda Za Ku Tsara Taswirar Sana'ar Ku Da Kanku Ku Samu Nasara

Tura Wannan Zuwa Ga

Babu wanda zai ba ka jari don ka fara sana’a ba tare da ka bayyana taswirar sana’ar ba dalla-dalla wato mene ne sana’ar, me za ta gabatar, su wane ne kwastomomi, yaya za’a tallata ta, wanne adadin lokaci za’a ɗauka kafin a fara samun riba, nawa ne adadin riba da za’a iya samu, nawa ake buƙata a fara, ta ya za’a samu riba, waɗanne irin matsaloli za’a iya shiga, da su wa ake gasa, ta yaya za’a samu nasara akan gasar da sauran batutuwa da yawa? Idan har kana neman jari, to ka shirya bayanai dalla-dalla musammam a rubuce domin nuna wa wanda kake so ya ba ka jarin.


Yadda Za Ku Tsara Taswirar Sana'ar Ku Da Kanku
Hoto: LinkedIn

MarubuciBello Galadanchi


Idan ya ga bayanan ka, to zai fi saurin gamsuwa har ya ɗauki jari ya ba ka. Musamman ma idan ya ga ka ɗauki lokaci ka rubuta duka waɗannan bayanan, zai yi tunanin cewa idan ka fara kasuwanci, to za ka lura da komai, kuma za ka bi komai dalla-dalla. Za’a fi yarda da kai. Idan ke matar aure ce ko budurwa da ke gidan su ko ke da saurayi mai albarkar aljihu, na tabbatar miki ki gwada ki gani, rubuta komai dalla-dalla, ki kai cibiyar kasuwanci ko business center a buga miki, ki miƙa masa ki ga ikon Allah. 

 

Taswirar kasuwaci mai kyau da kanta take sayar da kanta, musamman idan ta ƙunshi bayanai dalla-dalla akan binciken da ka yi da ilimin da ka tattaro dangane da wannan sana’a. Dole kuma taswirar ta ƙunshi yadda kake ganin sana’ar za ta bunƙasa a shekaru masu yawa, ba kawai ‘yan watanni ba ko shekara ɗaya ba ko biyu. 


Yana kuma da matuƙar muhimmanci wannan taswira ta bayyana duka irin matsalolin da za’a iya shiga, da ma wasu sana’a’o’in da za’a iya sauyawa idan ta farko ba ta yi nasara ba. 


Amma abu mafi matuƙar muhimmanci shi ne taswirar ta bayyana a fili shi ne babban dalilin da yasa sana’o’i suke karyewa shi ne rashin kuɗi. Duk da cewa ba shi zai iya taimakawa na wani ɗan ƙaramin lokaci, dolen dole sai sana’a ta samu kuɗin tafiyar da harkokin ta daga kuɗaɗen shiga da take samu. Taswirar kasuwanci mai kyau za ta iya yin lissafin irin kuɗaɗen da ake tsammani za su shigo a shekaru masu zuwa, da kuma bayyana inda ake tunanin za’a iya samun tsaiko.


Zama zakaran gwajin dafi wajen fara sana’a yana buƙatar jarumtaka da zuciyar ɗaukar sabon abu a saka a kasuwa, a nemi jari, a kuma yi amfani da ilimi da dabarun kasuwanci wajen aiwatar da shirin domin ganin sana’ar ta tsaya da ƙafafunta a shekaru da yawa masu zuwa, da kuma samun riba. 

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user