1. Ka fahimci za ka iya yin saɓani da mutane ba tare da ka zage su ko ka ci zarafinsu ba. Don mutane sun saɓa wa ra'ayinka, ba ka da damar ka ɗaga muryarka ko ka yi musu ihu.
2. Kai mutum ne mai karɓar laifinsa da ba da haƙuri idan gazawarka ta bayyana. Ba ka zargin wasu akan kuskurenka kuma kana ɗaukar alhakin abin da ka yi ɗari bisa ɗari.
3. Mutane za su iya yarda da kai su dogara da kai idan buƙata ta taso. Jama'a sun san ka sun san ɗabi'unka kuma za su iya bugun ƙirji akan halayenka na kirki da suka san ka da su.
4. Ba ka hukunta mutane bisa kamanninsu ko launin fatarsu. Ka gane cewa hasken fatar mutum ko kyawun suturarsa daban, kuma zuciyarsa da ɗabi'unsa su ma duk da daban.
5. Ka fahimci muhimmancin kauda kai da yafiya a rayuwa. Ka yarda da cewa ba duka abin da mutum ya ji ko ya gani zai tanka ko ya yi martani akai ba.
6. Ka fahimci cewa zaman lafiya ya fi zama ɗan sarki. Ka san muhimmancin zama lafiya da mutane, don haka kana girmama duk wanda ka yi mu'amala da shi kuma kana ƙoƙarin rabuwa da mutane lafiya.
7. Ka fahimci ƙarfafa wasu da taimakon su ba ya rage maka komai a rayuwa, sai dai ma ya ciyar da kai gaba. Kana yaba wa mutane a inda suka yi ƙoƙarin, tare da taimakonsu da ba su shawarwari na kirki.
8. Ka zama garkuwa mai bada kariya ga dukkan makusantanka. Ba ka bari wani ya yi zargi ko ya ci zarafin wani naka ko yana nan ko ba ya nan. Kana faɗin alkhairin da ka sani game da mutane kuma ba ka yarda a yi gulmarsu da kai a bayansu ba.
9. Ka daina damuwa domin mutane sun ce maka ba za ka iya yin wani abu ba saboda ka fahimci cewa suna faɗi ne saboda ƙaramin tunaninsu da gazawarsu ba naka ba.
10. Kana da buɗaɗɗiyar zuciya mai sauraron mabambantan ra'ayoyin ko sun ci karo da naka. Kana iya hulɗa da mutane da suka zo daga ƙabilu da al'adu da tushe daban-daban kuma ka zauna lafiya da kowanensu.
Allah Ya ba mu ikon zama lafiya da kowa Amin.
Tushe/Asali: Hausa Motivation