Sunday, 24 November 2024

Zafafan Kalaman Karfafa Soyayya Ga Masoyiya

Tura Wannan Zuwa Ga

Duk da cewa da akwai kyawawan 'yammata a duniya da yawa amma sai na ga kin yi musu zarra, ma'ana kin kere su wajen kyau da haɗuwa.


Zafafan Kalaman Ƙarfafa Soyayya Ga Masoyiya
Hoto: Next luxury

MarubuciImran Musa Jahun


Ke mai kyau ce, dole a ce kina da kyau, haka surar ki kyakkyawa ce wadda ko maƙiyinki ya san da hakan.


Ina son ki kodayaushe.


Rurutacciyar wutar ƙaunarki tana ci-gaba da ruruwa a zuciyata wanda hakan ya sanya son ki yake sake kwaranyuwa a cikin zuciyata.


Na ji son ki ne a take a yayinda idanuwana suka yi arba da tsaleliyar kyakkyawar fuskarki. 


Sai na ji bugun zuciyata yana fita da ƙarfi, dukkan wani kuzari na rasa shi, kin dolantar da ni sosai hakan ya sa na zama mara wayo.


Tauraruwarki ba za ta taɓa disashewa a zuciyata ba, abadan da'iman son ki yana tare da ni.


Haƙiƙa kin ɓoye ni a cikin hazo na so ta yadda ba na kallon kowacce 'ya mace sai ke. 

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user