Ina so na kwanta na yi bacci yanzu amma na kasa, kin san mene ne ya sa? Saboda tunanin ki ba zai bar ni na yi ba. Na rasa yadda zan yi da rayuwata saboda kowanne lokaci ƙwaƙwalwata tana cikin zunzurutun tunanin ki ne. Da fatan dai ke ma kina jin abin da nake ji a kanki?
Marubuci:- El-Nass
Na bincika zuciyata ciki da waje amma na rasa abinda nake ƙauna kuma zan ci-gaba da ƙauna har ƙarshen rayuwata idan ba ke ba.
Ina ƙaunar budurwa rantsattsiya ta ko'ina kamar ilimi, hankali, nutsuwa, tarbiyya da addini, iya kwalliya sannan da iya soyayya, a gare ki duk na samu waɗannan abubuwan da nake buƙata.
Ina so na zauna na ci abinci yanzu amma na kasa, kin san mene ya sa? A duk lokacin da na ɗauki kwanon abincin hoton ki nake gani kina mini murmushi.
Ke ce tauraruwa mai haskawa, na san ba za ki taɓa koɗewa ba, za ki zama fitila wacce za ta taimaka min na karanta taswirar zuciyata.
Rayuwata tana cikin ruɗani idan na wayi gari ban saki a idanuwana ba, zuciyata ba za ta iya jure zaman kaɗaici ba idan har ba ta tarar da ke ba, don Allah kada ki yi nisa da ni.
Ina matuƙar girmama soyayya a rayuwata, duniyar soyayya wata duniya ce mai cike da farin ciki da sanya shauƙi a zukata, na shiga wannan duniyar saboda ke ba na fatan fitowa daga cikin ta har abada.
Idan mutane goma suka kula da ke, ɗaya daga cikin su ni ne. Idan mutum ɗaya ya kula da ke, shi ma ni ne. Idan kuma babu wanda ya kula da ke, wannan yana nufin ba na cikin duniyar nan a raye.
Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum.