Saturday, 9 November 2024

Zantuttukan Karfafa Gwiwa Ga Wanda Ya Fidda Rai Na Cikar Burin Shi

Tura Wannan Zuwa Ga

Idan kana da burin da kake son cimmawa, sai kuma ya zama abokai da makusanta ba sa mara maka baya, to ka sani ba haƙƙin ka ba ne a kansu sai sun mara maka baya, duk da cewa ya kyautu su yi hakan, hasali wannan jarrabawa ce mai fayyace cancantar ka a kan wannan buri ko akasin haka.


Zantuttukan Karfafa Gwiwa Ga Wanda Ya Fidda Rai Na Cikar Burin Shi
Hoto: Psychowellness center

Marubuci:- Buzu Danfillo


Shin za ka iya tsaya wa kanka yayin da hatta na kusa da kai sun yi wasarere da mafarkin ka ko burin ka? Ko kuma nasarar ka ta raja'a ne a kan ra'ayoyin waɗanda ba su da fahimta ko ilimi akan abun da ka sa a gaba? Wannan jarrabawa ba tsakanin kai da su ba ne, tsakanin kanka da kanka ne.


Za ka iya hawa hanyar muradin ka kai kaɗai ko sai da 'yan rakiya?


Yadda ba dole ba ne sai sun mara maka baya, kai ma ba dole ba ne sai ka yi da su, ba a shafi ɗaya kuke ba, hakazalika ba amo ɗaya kuke yi kai da su ba, don haka ba za ku taɓa fuskantar juna ba.


Yayin da ƙasa ta ƙi karɓar shuka ba shukar ake sauyawa ba, ƙasar ake sauyawa don haka idan mafarkin ka ko burin ka ya ƙi shukuwa a ƙasar gaban ka, to tuge shukarka ka nema mata ƙasar da za ta girmar da ita, babu riƙo ba ƙullaceceniya. 


Sai dai zuwa gaba idan ka yi nasara, kada ka ba kowannen su damar haskawa tare da kai wato shining da kai. Irin "Ai wane ga gidan mu ga gidan su". Ɗin nan. Kawai ka fuske irin na rashin ganewa ɗin nan, ehi.


Waɗanda suka fi mu ci gaba a duk faɗin duniya ba basira ko baiwa suka fi mu ba, tsari, ɗabi'a da ɗa'a suka fi mu.


Baiwa da Fikira ba su da al'umma, addini, jinsi, ƙabila, yare/harshe ko ƙasa. Lamunci hakan ka samu sa'ada.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user