Friday, 15 November 2024

Zazzafar Wasikar Soyayya Ga Nafisa

Tura Wannan Zuwa Ga

Assalamu Alaikum Nafisa, ya kike ya harkokin soyayyarki suke? Ya gurin aikin ki? Ina fatan komai yana nan lafiya. Nafisat ki saka wannan a zuciyarki cewar soyayyata a gare ki ba ta da ranar ƙarewa domin kuwa kin gina soyayyarki ne a cikin zuciyata kuma na sallama miki dukkanin zuciyata.


Wasikar soyayya zuwa ga Nafisa
Hoto: Liubomyr Vorona/Dreams time 

Marubuci:- El-Nass


Na sha ganin mata a duniyar nan da suka shiga raina sosai har na furta musu kalmar soyayya amma ban san na yi kuskure ba sai da na haɗu da ke a lokacin na ji babu abin da nake so a duniya idan ba ke ba, kuma zan ci gaba da son ki har abada.


Sarauniyata babu wani abu da yake da muhimmanci a duk lokacin da ba ki tare da ni, Nafisat idan har ba na tare da ke komai nawa zai yamutse ne. Ke ce jin daɗina, ke ce farin cikina, sannan kuma ke ce komai nawa.


Nafisat, idan har ina tare da ke ina jin matuƙar farin ciki. Na yi matuƙar farin ciki da na same ki a matsayin sarauniyar zuciyata.


Kin sanya zuciyata ta zama ƙarfaffiya. Zan ci-gaba da son ki ne da ɗaukacin dukkanin zuciyata.


Ina son ki, daga masoyinki  El-Nass.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user