Monday, 30 December 2024

Abubuwa 5 Masu Gyara Rayuwar Matashi

Tura Wannan Zuwa Ga

Abubuwa biyar yana da kyau duk wani matashi ya sani kuma ya kiyaye su. Idan kai matashi ne ya kamata ka san waɗannan abubuwa biyar ɗin.


Ga su kamar haka:


 1. Lokaci


A halin da kake kana cikin wani lokaci ne wanda Allah ya ware maka na musamman a rayuwarka, ƙarfin ka ya kai ƙarfi, tsokar jikinka da gaɓoɓin jikinka duk suna nan lafiya, sannan ƙwaƙwalwarka na saurin yanke shawara.


Ƙaramin yaro ba zai samu wannan damar ba, sannan tsohon mutum ba zai samu ba sai kai.


Abubuwa 5 Masu Gyara Rayuwar Matashi
Hoto: Adobe Stock

Marubuci:- Khalid A Gombe


Duk abin da za ka nema ka neme shi a wannan lokacin kada ka bari lokacin ya wuce maka. Da zarar ka kai shekaru 20 to kana da sauran shekaru 20 da Allah ya albarkace ka da su.


Ka nemi duniyarka da lahirarka ba tare da  gajiya ba.


2. Abokai


Ka zagaye kanka da abokai nagari waɗanda suke da natsuwa. Zama da mutum na gari zai sanya ka zama nagari.


Duk yadda mutumin banza yake son ka da abota kada ka sake ka yi abota da shi. Ka yi abota da mutanen da suka yi nasarar rayuwa, kai ma za ka yi nasara.


3. Zamani


Ka kula da zamani sosai domin shi ne abin da ya fi ruɗar mutane. Idan ka ga ana yayin wani abu sai ka ji kana son mallakar abin.


Kada ka mallaki abu don kawai ana yayin sa ko don ka burge wani, ka mallaki abu domin kana da buƙatar abin kuma domin amfanin da abin zai maka.


4. Ka maida hankali


Kada ka zama mai sa'ido akan harkokin wani maimakon haka ka maida hankali wajen tafiyar da naka harkokin.


Matuƙar kana so ka ci gaba to dole sai ka daina shiga abin da bai shafe ka ba. Ka yi ƙoƙarin gano laifinka kuma ka gyara laifin ya fi ka dinga bincikar laifin wani.


5. Haƙuri


A duk abin da kake nema to ka sani haƙuri ne kaɗai zai ba ka abin.


Kada ka damu don abokanka sun riga ka samun arziki kai ma naka na zuwa a lokacin da ya dace.


Wani zai iya riga ka aure kuma ka riga shi haihuwa haka wani zai riga ka samun arziki amma ka zo ka fi sa arzikin. Don haka ka kwantar da hankalinka lokacinka zai zo.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user