Mafiya yawancin matsalolin mu ba wai ba su da magani ba ne ba, a'a mu ne dai muka kasa neman maganin nasu.
Marubuci:- Abdulfatah Yakubu
Kamar yanda jirgin ruwa ba zai iya tafiya akan sahara ba, haka zalika su ma matsalolin mu ba za su iya magance kansu da kansu ba dole sai mun yi wani abu akai.
Komai na rayuwa a tsare yake, sharaɗin magance yunwa shi ne mutum ya ci abinci, sharaɗin korar jahilci kuma mutum ya nemi ilimi, hatta likita ba zai ɗora ka akan magani ba har sai ya gano matsalar ka.
Masana falsafa suna cewa;
من الوارد أن تكون كل مشكلتك أنك لست في المكان المناسب.
Akwai yiwuwar cewa babbar matsalar ka ba komai ba ce face kasancewa a inda bai dace da kai ba.