Sunday, 8 December 2024

Dalilai 3 Da Su Hana Ka Cimma Nasara

Tura Wannan Zuwa Ga

Dalilai uku da suke zama tarnaƙi ga samun nasara a rayuwa.


Ga su kamar haka:


1. KARAYAR ZUCIYA DA HANGEN GAZAWA


Wani lokacin mutum da kansa ya kan karya zuciyarsa da jin cewa wani abu ba mai yiwuwa ba ne a wajensa, ba kuma tare da ya gwada ba.


Dalilai 3 Da Su Hana Ka Cimma Nasara
Hoto: Freepik

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Wani kuma wasu ne za su nuna masa cewa abu kaza ya fi ƙarfin sa. Daga nan sai ya ɗauka koda ya gwada ɗin ba zai yi nasara ba.


Abin da bai gane ba shi ne, da yawan lokaci Ɗan Adam ba ya sanin ƙarfin sa, har sai ya gwada tukunna.


Kada ka karya zuciyar ka akan komai, kuma kada ka saurari wanda ba zai ƙarfafa maka gwiwa ba.


2. LALACI DA NEMAN SAUƘI


Wannan ba ya buƙatar fassara da yawa, domin kowa ya san illar lalaci, sai dai ba kowa ne ya fahimci cewa, neman sauƙi a cikin komai na iya zama tarnaƙi ga ci-gaba ba.


Denzel Washington yana cewa; Sauƙi ya fi zama tarnaki ga ci-gaba sama da tsanani.


"Ease is more threat to progress than Hardships."


Masu hikima kuma suka ce; Tsanani na haifar da jarumta. Ita kuma jarumta tana kawo mafita. Mafita kuma tana kawo sauƙi.


Ka ga kenan idan kana kwance kawai, kana neman sauƙi, ba za ka zama jarumi ba, ballantana ka samo mafita, wadda ita ce ke kawo sauƙi.


3. KWAƊAYIN GIDA DA TSORON SAUYI


Bahaushe yana cewa sabo turken wawa, ma'ana wanda ya kasa barin abin da ya saba da shi, ya kuma karɓi wani yanayi sabo domin ci-gaban sa, to ya yi wauta.


Da yawa mutane ba sa son barin gida ko sauya fasalin rayuwar su, domin samun ci-gaban da suke buƙata.


Hakan kuma ba ƙaramin tarnaƙi ba ne ga samun nasara, dole wani lokacin sai ka bar gida, ko sauya fasalin rayuwar ka, kafin cimma burin ka.


Allah yasa mu dace Amin.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user