Da yawan mutane suna yi wa kansu wasu tambayoyi a zuciyar su kamar haka;
Yaushe zan yi kuɗi ne?
Me ya hana ni yin kuɗi?
Anya kuwa zan yi kuɗi?
Abinda da yawan mu ba mu fahimta ba shi ne, samun kuɗi fa ko rufin asiri sai ka shirya hakan tun daga zuciyar ka.
Marubuci:- Bello Ado Hussaini
Wasu za su ce wannan maganar ai ba Tauhidi, kuɗi ƙaddara ce kawai.
Eh komai muƙaddari ne daga Allah (S.W.T), shi ne mai bayarwa kuma mai hanawa amma duk mai shekaru irin namu, daga 40 zuwa sama, idan ya tsaida hankalin sa, zai yadda cewa cikin shekarun da ya yi a baya, Allah (SWT) ya ba shi wata dama komai ƙanƙantar ta, yadda zai yi kuɗi ko ya samu rufin asiri.
Sai dai kash ya aikata ɗaya daga cikin waɗannan kurakurai guda 3, ko ma dukansu, shiyasa har yanzu yake cikin talauci.
MENE NE WAƊANNAN KURAKURAI GUDA UKUN?
1. Kana yin sana'a, amma a cikin zuciyar ka ba ka son ta, kana yin ta ne a matsayin ta wucin gadi (temporary) kafin wata sana'ar da kake hange ta samu.
Illar hakan shi ne, wannan sana'ar ba za ka taɓa yi mata tsari ba, ballantana ka gina wani abin kirki a cikin ta, domin hankalin ka ba ya kanta, kawai dai kana yi ne, ba sha'awa ba dogon buri.
Don haka ba za ka godewa abinda kake samu daga gare ta ba, har ka yi tunanin tattali da bunƙasa ta.
2. Kana sana'a kuma kana sha'awar ta, amma ka raina abinda take ba ka, har kana ganin cewa, wannan sana'ar ina mutum za shi da ita? Ɗan wannan abin da ake samu wane tanadi mutum zai yi, har ya gina wani abin arziki amma fa a daidai lokacin da kake yi wa sana'ar taka kallon ƙarama mara riba, 'yar fulani mai siyar da fura da nono a kasuwar sabon gari, ta tara miliyan shida (6 million) ta biya kuɗin Aikin Hajji da wannan cinikin furar, ba wai saniya ta siyar ba.
Ka ga ashe ba ƙanƙantar abin da kake samu ba ne, tsari ne da juriya da tarbiyya, wato horarwa.
3. Kana yin sana'a, kuma kana samun kuɗi gwargwadon hali, wanda sun isheka buƙatun rayuwa.
Sai dai ba ka da linzami wajen kashe kuɗi da buƙatu marasa dalili.
Duk buƙatar da ta zo gaban ka yin ta kake yi. Ka ɗorawa kanka wani ma'auni wato tsayayye, kai lallai sai ka rayu haka, ba za ka jira lokaci ba.
Kai ne canja waya sabuwar shigowa, duk bikin da aka gayyace ka sai ka sa sabuwar riga.
Ko yaya wani abu ya karci motar ka ko babur ɗinka, sai ka je gareji.
Duk sati sai ka je Carwash an yi maka General.
Da yawan mu a wannan ajin muke, shiyasa kuɗin mu bai taru ba.
Kai kanka ka zauna ka yi lissafi idan za ka iya, a cikin 2024 ɗin nan, duk da azabar Baba Bala Blu, nawa ka samu daga Janairu zuwa Nuwamba? Wallahi za ka tarar kuɗaɗe ne masu yawa.
Amma ka gayawa ranka ai ƙasa ta rikice, ya za'ayi ma mutum ya tara kuɗi? Don haka ka cinye kuɗin ka ba tare da ka lura ba.
Mafita ita ce, komai ƙanƙantar abin da kake samu, za ka iya yin tattali ka tara don gobe.
Za ka iya haƙura da wasu buƙatun na dole, ka jure wahala, domin gobe ka samu farin ciki da arziki mai ɗorewa, maimakon yau akwai, gobe babu.
Mutum nawa ne suke ƙin cin abinci a kasuwa sai kame-kame, kuma da kuɗi a jikinsu, sai sun dawo gida.
Mutum nawa ne suka ajiye abun hawan su, su hau keke napep, kuma sun fika samun kuɗi.
Mutum nawa ne suke riƙe waya ɗaya shekaru 3 ba canji, kuma sun fika samun kuɗi.
Amsar ita ce, duk abin da kake son cimma a rayuwa, sai ka yi sadaukarwa.
Sai ka jure wata wahala domin ka ji wani daɗin.
Sai ka yi tanadin yau domin gobe.
Allah ya sa mu gane wannan karatun, har da ni don ni ma so nake na yi maza na yi kuɗin nan kafin Nigeria ta gama rikicewa.
Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.