Abokina kada ka damu don ka rasa wanda zai kula da kai a rayuwa, domin mutane da dama sun kasa kulawa da kansu ma ballantana kuma har su kula da wani, kai dai kawai ka damu da kanka.
Marubuci:- El-Nass
Mutanen kirki tamkar bishiyar mangwaro suke, a yayin da kake jifansa shi kuma a lokacin yake sako ma 'ya'yan shi masu zaƙi domin ka sha.
Kada ka zama mai ƙyashi da hassada ga samun wani, domin ba za ka mutu ba har sai ka samu duk abin da Allah ya yi nufi za ka samu a duniya.
Ba laifin ka ba ne ka zama mummuna ta fuskar halitta, ko ka zama talaka domin ba kai ka yi kanka ba, Allah ne ya so ya gan ka a haka amma laifin ka ne ka zama mai mummunan hali domin hali shi ne mutum.
Mace na iya yafe maka duk laifin da kai mata amma ban da laifi ɗaya wato shi ne laifin rashin ba ta kulawa ta fuskar soyayya.
Ni ma anan zan iya yafewa duk wanda ya yi mini laifi ta fuskar zamantakewa amma ban da cin amana.
Duk wanda ya ce zo mu zauna to masoyinka ne kada ka sake shi.
Kada ka damu don ka rasa wani abu mai kyau wanda kake so, sau da yawa sai ka rasa abu mai kyau sannan kake samun mafi kyau.
Ka zama mai ra'ayin kanka domin ka rayu a kan abinda kake so, idan har ka rayu akan ra'arin wani har ka mutu burinka ba zai cika ba domin kuwa ba ka rayu akan ra'ayinka ba.
Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.
Allah ka ba mu abokan zama na gari Amin.