Bayan dubun gaisuwa mai fesar da tsantsar so da ƙauna, mara misaltuwa, jinjina da yabo da kirari su ƙara tabbata a gare ki yake burin zuciyata, fatana shi ne mallakarki a matsayin uwar 'ya'yana abar alfaharina, burina mu kasance tare ba na fatan rasa ki domin muhimmancin ki a gare ni.
Marubuci: Imran Musa Jahun
Zuciyata da ruhina suna azabtuwa ta dalilin son da nake miki, ƙishin ruwan son ki ya gallabi dukkan ilahirin sansanin zuciyata na rasa yadda zan yi, domin samun sassauci daga raɗaɗin da zuciyata ke faman yi shi ne nuna soyayyar ki a gare ni, rashin samun haka daga gare ki kan iya janyo barazana ga rayuwata.
Na ɗauki alƙawarin samar miki da farin cikin zuciyar ki, ba zan taɓa sa wa ki ji ba daɗi a cikin zuciyar ki ba. Ina son ki.
Ke na ba mulkin zuciyata ki mulke ta yadda kike so taki ce kuma mallakin ki ce.
Ina son ki, ina ƙaunar ki ba na fatan rabuwa da ke, saboda irin son da nake miki.
Rashin samun soyayyar ki a gare ni zai iya zama silar faruwar komai, burina shi ne ki ba ni dama domin nuna miki soyayya ta haƙiƙa.
Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.