Friday, 27 December 2024

Gajerun Kalaman Soyayya Masu Kara Kauna Ga Masoyiya

Tura Wannan Zuwa Ga

Ya abar ƙaunata, soyayya idan ba taki ba ƙarya ce, son ki ba zan daina ba. Idan na gan ki ko na ji muryarki sai na ji dukkan wani ƙunci ya tafi.


Gajerun Kalaman Soyayya Masu Ƙara Ƙauna Ga Masoyiya

Marubuci:- Sadik Ebra


Aminci a gare ki ma'abociyar hankali da tunani, babu shakka ke ce sinadarin da ke sarrafa tunani na a kodayaushe.


A gaskiya ina sonki, babban burina na aure ki, cutar son ki ba ta da magani a gurin likita, daɗaɗan lafazinki kan sanyaya mini zuciyata, ɗebo zumar son ki ki shayar da ni, tsaftatacciyar fuskarki ke haskaka zuciyata, hanzarta ki dilmiya ni cikin kogin son ki.


Masoyinki shi ya cancanta ya mallaki mulkin rayuwarki, na san ba ki da shakka ko tantama ga son da nake miki.


Kin makantar da idanuwana, kin sa ba na ji kuma ba na ganin wata 'ya mace sai ke.


Ke ce ma'abociyar yalwar gashin gira da ƙyallin haƙori da lotsawar ƙunci wanda idan kika yi murmushi na kan ji tamkar wanda daɗi ya yi masa yawa a duniya.


Yake fitacciyar sarauniyar zuciyata wacce ba zan taɓa mantawa da ke ba a bangon zuciyata.


Ya kyakkyawar jarumata ba ni da wacee nake so face ke.


Ƙarin abin sha'awa a ce na mallake ki watarana, rayuwata za ta yi rauni matuƙar na rasa samun ki, ke ce uwargida mai ran ƙarfe burin ƙalbina.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user